✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

JAMB 2022: Dalibai 378,639 sun samu sama da maki 200

JAMB ta ayyana maki 140 a matsayin mafi karancin domin samun gurbin karatu a jami'a, maki 100 kuma ga kwalejin fasaha da na ilimi.

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta bayyana cewa dalibai 378,639 kacal ne suka samu akalla maki 200 daga cikin dalibai 1,761,338 da suka rubutarta (UTME) a 2022.

Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya bayyana haka da cewa hukumar ta ayyana maki 140 a matsayin mafi karancin domin samun gurbin karatu a jami’a, maki 100 kuma ga kwalejin fasaha da na ilimi.

Da yake jawabi a wani taro da Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya jagoranta a Abuja ranar Alhamis, Oloyede ya ce dalibai 378,639 ne suka samu akalla maki 200 a jarabwar UTME ta bana.

Ya ci gaba da cewa dalibai 520,596 kuma sun samu akalla maki 190, wasu 704,991 kuma akalla maki 180, sai 934,103 suka samu maki akalla 170, sannan 1,192,057 suka samu maki akalla 160.

Ya ce, hukumar ta bai wa daliban da ke jiran sakamakon kammala sakandare damar yin rajistar da zana jarrabawar UTME ta 2022.

“JAMB ta kyale masu jiran sakamakonsu sun yi rajista da kuma rubuta UTME ta 2022.

“Amma wadannan dalibai ba za a ba su gurbin karatu ba tare da sakamakon ba.

“Dole sai sun sanya sakamakonsu na kammala sakandare a manhajar JAMB kafin a fara bayar da gurbin karatu,” inji shi.