✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jama’ar gari sun kona barawon babur kurmus

Rundunar ’yan sandan jihar ta yi jan kunne kan masu daukar doka a hannu.

Wani da ake zargi da satar babur da wani dan kungiyar asiri sun hadu da ajalinsu a garin Makurdi na Jihar Binuwai.

Wani shaida ya bayyana wa Aminiya cewa barawon ya gamu da ajalinsa ne bayan ya kwace wa wani dan acaba babur a Demekpe da ke yankin Wadata a garin Makurdi.

  1. Borno: Sojoji sun dakile mahara a garin Auno
  2. Yadda za a samu fatar fuska mai sulbi

Ipole, wanda lamarin ya faru a kan idonsa, ya ce barawon yana kokarin tserewa ne asirinsa ya tonu.

Kafin kiftawa da Bismillah gungun wasu matasa da ’yan acaba suka tare shi suka banka masa wuta ya kone kurmus.

Makamancin hakan ya kuma faru a daidai Babbar Kasuwar garin Makurdi a ranar Juma’a, inda aka yi wa wani mutum kisan gilla.

Wakilinmu ya rawaito cewar wani dan kungiyar asiri ne ya biyo mutumin yana harbin sa amma harsashin bai same shi ba.

Wani ganau ya ce a bainar jama’a abokan hamayyarsa suka yi gunduwa-gunduwa da shi, wanda hakan ya jefa mutane cikin rudani.

Kakakin ’yan sandan Binuwai, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, sannan ta yi gargadi kan aikata muggan laifuka.

“Lamarin ya faru amma mun yi Allah wadai da faruwarsa,” a cewar Anene a sakon waya da ta aike wa wakilinmu.