✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jama’ar gari sun kashe ’yan bindiga 13 sun kona su a Sakkwato

Mutanen Tangaza sun fito don kare kansu daga ramuwar gayyar ’yan bindiga.

Jama’ar gari a Tangaza, Jihar Sakkwato, sun yi wa wasu ’yan bindiga 13 dirar mikiya sun kashe su sannan suka kona gawarwakin.

Jama’ar garin sun damko ’yan bindigar ne a babban ofishin ’yan sandan da ke garin a ranar Asabar, suka aika su lahira nan take kuma suka banka wa gawarwakin wuta.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

An cafke ’yan bindigar da aka yi wa kisan gilla ne bayan sun kai wa garin hari ranar Juma’a da dare, inda suka kashe mutum biyu, ciki har da wani dan tireda da suka yi awon gaba da kayan abinci daga kantinsa.

A lokacin harin, ’yan bindigar sun tilasta wa wasu mutum biyu ’yan garin su yi musu dakon kayan da suka kwasa zuwa cikin daji, amma kuma suka kashe mutanen bayan sun kai musu kayan.

Bayan nan ne hadin gwiwar jami’an tsaro da ’yan banga suka yi sammakon kai samame a dajin Tangaza, inda suka yi nasarar cafke ’yan bindiga 13  har da kayan abincin, suka kawo su Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke garin Tangaza.

Wani mazaunin garin ya ce a lokacin da aka kawo ’yan bindigar da aka kama ne fusatattun mutanen garin suka sha karfin jami’an tsaron, suka yi wa ’yan bindigar dirar mikiya suka kashe su gaba daya suka kuma banka wa gawarwakin wuta.

Ya shaida mana cewa a halin yanzu jama’ar garin sun yanke shawarar fitowa kwansu da kwarkwata domin su kare kansu daga yiwuwar harin ramuwar gayya daga ’yan bindiga, “Sannan an kawo mana karin jami’an tsaro an girke a yankin”.

Wani mazaunin garin ya ce ’yan bindigar da aka kashe sun kai 16.