Mutanen gari sun hallaka mutum daya da ake zargi da garkuwa da mutane suka kuma lahanta dayan a Jihar Sakkwato.
Dandazon mutanen sun kuma kona Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Karamar Hukumar Kware ta Jihar inda aka tsare mutanen da ake zargi da satar mutane.
- ‘Jami’an gwamnati na wa jami’an tsaro manakisa a yaki da ta’addanci’
- An cafke Basarake da iyalansa kan zargin garkuwa da mutane
- Majalisa ta nemi Buhari ya ayyana dokar ta-baci a Najeriya
- Ronaldo ya gindaya sharadin rabuwa da Juventus
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ta ce gungun mutane sun yi wa ofishin ’yan sandan tsinke ne suna neman a damka musu wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Kakakin Rundunar, ASP Abubakar Sanusi, ya ce ana tsaka da bincikar wadanda ake zargi ne mutane suka fara boren a ofishin ’yan sandan cewa dole a mika musu wadanda ake zargin.
Da haka ne zugar mutanen suka fi karfin jami’an da ke ofishin ’yan sandan, suka kona ofishin da motocin ’yan sanda da ke ajiye a wurin.
Ya tabbatar da cewa mutanen suna sun kashe daya daga cikin wadanda ake zargin, dayan kuma suka ji masa rauni.
Sai dai ya ce ba a kama kowa ba, amma ana kan gudanar bincike a kan lamarin.