A Kyiv babban birnin Ukraine, jin karar fashe-fashe da kuma jiniya da ke ta tashi, sun sa mazauna birnin sun shiga firgici, inda suke ta in-ba-ka-yi-ba-ni wuri, wajen neman mafaka a tashoshin jirgin kasa.
Haka kuma jama’a sun layi a wuraren cirar kudi na banki, da gidajen mai da manyan kantunan sayar da kayan masarufi.
- Kasuwannin duniya sun tafka asara bayan Rasha ta shiga Ukraine da yaki
- Rikicin Ukraine: Gwamnatin Tarayya za ta gaggauta dawo da ’yan Najeriya gida
Wannan dai na zuwa ne a yayin da ‘yan Ukraine din suka wayi gari da abin da suka dade suna jin tsoro na harin na Rasha, can kuma a wasu sassan kasar, cuncurundon ababen hawa ne ake gani na wadanda suke kokarin ficewa.
BBC ya ruwaito mai magana da yawun fadar shugaban kasar yana cewa Rasha na so ta ribaci firgicin da ta jefa fararen hula ne kawai, yana mai shawartar jama’a da kada su karaya.
To amma wannan ga alama bai kwantar da hankali ba, domin tuni wasu ’yan kasar suka fara tsallaka iyakar kasar ta Kudu maso Yamma zuwa cikin Romania domin samun mafaka.
Ita ma Poland tuni ta samar da wurare takwas na karbar mutane, ko da za a fara neman tsira, inda za ta samar da abinci da kula da lafiya da kuma samar da bayanai.
Kafafen watsa labarai a Moldova sun bayar da rahotannin gomman motoci da ke layi a kan iyakarta da Ukraine din.
An sanya dokar hana fita a birnin Kyiv
A ’yan awannin da suka gabata ne Magajin Garin birnin Kyiv, Vitaliy Klitschko ya sanar da dokar hana fita a fadin birnin.
Ya ce: “Jama’a! Kyiv na gabatar da dokar hana fita daga yau. Za ta fara aiki daga tsakanin karfe 10 na dare zuwa 7 na safe a kullum.
“Hakan ya zama dole saboda tsaron al’ummar birnin a yayin da ake tsaka da rikicin soji.”
Motocin haya ba za su yi aiki ba a yayin da dokar ke aiki, amma jiragen kasa za su ci gaba da aiki a matsayin mafaka.