Wasu mazauna unguwannin Kaduna sun koka da tsarin karin kudin wutar lantarki da aka fito da shi.
A cewarsu, a wasu unguwanni ba a samun wutar sosai amma sai ga shi an yi karin kudin wutar.
Malam Umar Ramalan wanda mazaunin unguwar Badarawa Malali ne a jihar ya ce, “Gaskiya tsarin bai yi ba domin a yanzu fa mutane na hannu baka ne hannu kwarya.
“Kuma kwatsam sai ku ce an kara wutar lantarki. Da wanne za mu ji, da neman kudin abinci ko da na kudin wuta?
“Gaskiya da akwai bukatar gwamnati ta sake duba lamarin”, inji shi.
Shi ma Badamasi Isah wanda mazaunin Unguwar Dan Mani ne ya ce gaskiya abin bai masu dadi ba.
“Gaskiya ba mu ji dadin wannan karin ba duk kuwa da cewa muna samun wuta a unguwarmu sosai.
“Amma dai unguwar talakawa ce kuma mutane da yawa ba za su iya biyan wannan kudi ba”, inji Badamasi.
Yadda tsarin karin kudin yake
Sai dai har yanzu jama’a basu fahimci yadda tsarin karin yake ba.
Hakan ce ta sa Aminiya zantawa da kakakin kamfanin raba wutar lantarki a Jihar Kaduna Abdul’azeez Abdallah.
Ya ce an tsara Karin ne mataki-mataki ta yadda akwai wadanda za su samu wuta na tsawon sa’oi 20 zuwa sama a unguwanninsu sannan akwai ’yan kasa da sa’oi 20”, inji Abdul’azeez.
Iya wutarka iya kudinsa
Jami’in ya ci gaba da cewa, “Karin kudin ya bambanta domin iya wutan da ka sha shi za ka biya.
“Idan a unguwarku kuna samun wuta fiye da sa’a ashirin kudin zai karu fiye da wanda ba su samu yawan wannan sa’oi.
“Yawan wutarka yawan abin da za ka biya saboda ba tsari ne da aka yi na bai-daya ba.
“Kuma saboda unguwannin na da yawa shi ya sa muka fito da abin mataki-mataki. Iya wutan unguwarku iya kudin da za ku biya.
Kowa zai san matsayinsa
“Ta haka ne mutane za su fahimci wane tsari suke a kai.
“Idan ka je karbar bil (takardar kudin wuta) dinka za a rubuta maka matakin da kuke a unguwarku, Ko idan kaje sayen katin mitarka shi ma za a rubuka maka.
“Abin sha’awa a nan shi ne za a samu karin sa’o’i na wuta a unguwanni sai dai kuma jama’a za su biya karin kudi a kan abin da suke sha ne kurum”, inji jami’in.