Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Mohammmed Adamu ya umarci jami’an rundunar da su guji amfani da karfi a kan masu zanga-zangar lumana.
Kashedin da kakakin Rundunar, Frank Mba ya fitar ta ce ’yan Najeriya na da ’yancin bayyana ra’ayi da kuma gudanar da taruka da sauran harkokinsu.
- Rashin tsaro: ’Yan daba sun kai wa masu zanga-zanga hari a Kano
- An haramta zanga-zangar #EndSARS a Abuja
- #EndSARS: Sojoji sun yi wa masu tayar da rikici kashedi
- #EndSARS: Sojoji sun yi wa masu tayar da rikici kashedi
Don haka ya ce wajibi ne jami’an rundunar su kiyaye tare da kare wadannan hakkoki na ’yan kasa.
Ya kuma roki masu zanga-zangar #EndSARS da su gudanar da ita cikin lumana sannan kar su ba da dama bata-gari su saje da su.
Shugaban ’yan sandan ya yi wa musu alkawarin yin dukkan mai yiwuwa wajen magance kokensu na neman gyaran rundunar.
Ya ce aikin zai kawo gyaran da zai kyautata dangantaka tsakanin ’yan sanda da jama’a tare da hukunta dukkan jami’an da aka samu da laifi.