✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jahilai ne ke juya al’amuran siyasa da gwamnati a Kano — Hadimin Ganduje

Tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na Jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji, ya ce masu fama da duhu na jahilci ne ke juya akalar al’amura na…

Tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na Jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji, ya ce masu fama da duhu na jahilci ne ke juya akalar al’amura na siyasa da jagorancin al’umma a Jihar Kano.

Injiniya Mu’azu wanda ake yi wa lakabi da Dan Sarauniya, ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa kan shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 12 ga watan Janairun 2021.

A sakon nasa, ya bayyana damuwa dangane da yadda wasu marasa ilimin addini da na zamani ke cin karensu babu babbaka wajen jagorantar al’amura na siyasa a Kano duk da cewa akwai tarin Malamai kuma shi kansa Gwamnan Jihar, Abdullahi Ganduje yana da shaidar karatu ta digirin digirgir wato PhD.

Ya wallafa cewa, “Jahilci ba ado bane, illa ne ga rayuwa, ci gaba da zaman lafiyar al’umma.”

“Jiha kamar Kano, mai PhD Gwamna, mai ilimi da Malaman addini, a ce wasu tantirai…ba Arabi ba Boko ne ke juya akalar lamuranmu a siyasa da rayuwa! Da sake!”

Sakon da Injiniya Mu’azu Magaji ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ana iya tuna cewa, Gwamna Ganduje ya sauke Dan Sarauniya daga kujerar Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na Jihar Kano bayan ya wallafa wani sako a shafinsa na Facebook da ake zargin yana murna da rasuwar Mallam Abba Kyari, tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.

Daga bisani bayan ya nemi afuwa kuma ya yi karin haske kan hakikanin ma’anar sakonsa da ya wallafa, Gwamna Ganduje ya sake ba shi mukami a matsayin Shugaban Kwamitin da zai jagoranci ayyukan samar da Bututun Iskar Gas a Jihar Kano.