A yau Asabar 12 ga Satumban 2020, za a fara fafata Gasar Firimiyar Ingila ta bana, tsakanin kungiyoyin kwallon kafa 20 wadanda uku daga ciki sabbi ne a yayin da suka samu nasarar haurowa daga rukunin Gasar Championship.
Kungiyoyin uku da suka hauro sun hadar da; Leeds United da West Bromwich Albion da kuma Fulham United.
A bana dai Kungiyar Leeds United za ta dauki hankalin ’yan kallo saboda yadda ta shafe shekara 17 rabonta da Gasar Firimiya wadda kuma ake yi mata kallon kungiyar da za ta tabuka abin a zo a gani duba da yadda take da kwararren mai horaswa.
Akwai kuma kungiyar Chelsea wacce ita ma ’yan kallon za su maida hankali a kanta saboda sayen manyan ’yan wasa da ta yi a bana irinsu Hakim Ziyech, Timo Werner, Kai Havertz da sauransu.
- Ya yi wa dalibarsa fyade a aji tana tsaka da rubuta jarrabawar WAEC
- Ramin da titin Kaduna ya yi ya sake ruftawa bayan gyara
Tun da fari an dage wasan da Burnley za ta fafata tsakaninta da Manchester United, sai kuma wasan Manchester City da Aston Villa wanda shi ma an dage zuwa nan gaba.
Za a fafata wasa ranar Asabar 12 ga Satumba tsakanin Kungiyar Fulham da Arsenal da misalin karfe 12 da rabi sai wasan Crystal Palace da Southampton wanda za a fafata da karfe 3 na rana.
Liverpool da Leeds United za su yi nasu gumurzun da misalin 5 da rabi na yamma sai kungiyar West Ham da Newcastle da karfe 8 na dare.
A wasannin ranar Lahadi 13 ga Satumba, za a kece raini tsakanin West Brom da Leicester City da karfe 2 na rana sai wasan Tottenham da za ta karbi bakuncin Everton da misalin karfe 4 da rabi na yamma.
Wasan Litinin 14 ga Satumba: Sheffield United za ta kara da Wolves da karfe 6 na yamma sai wanda za a buga tsakanin Brighton da Chelsea da misalin karfe 8 da rabi na dare.