✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayen ’yar shekara 3 da ta mutu sanadiyar fyade na neman hakki

Mahaifiya marigayiyar ce ta gano gaban ‘yarta na jini a lokacin da ta zo yi mata wanka.

Iyayen wata yarinya ‘yar shekara 3 da ake zargin ta mutu sanadiyar fyade, na rokon da a bi musu hakki.

Iyayen yarinyar na zargin wani dan shekara 45 da yi wa ‘yarsu fyade ne da hakan ya kai ga mutuwarta.

Ana zargin mutumin ne da aikata laifin a ranar Litinin 26 ga watan Satumbar 2022, a Lungun Mai ruwa da ke unguwar Gama a Karamar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.

‘Yan sanda sun kama wanda ake zargi bayan shigar da kara da mahaifin yarinyar ya yi a ofishinsu a ranar 29 ga watan Satumbar 2022.

Mahaifiya marigayiyar ce ta gano gaban ‘yarta na jini a lokacin da ta zo yi mata wanka, da ta tambaye ta, sai yarinyar ta sanar da ita sunan wanda ya yi mata wani abu, kuma ya ce zai kashe ta, ya kuma ba kyanwa namanta idan ta fada.

Marigayiyar ta ce wanda ake zargin ya kan kai ta wani daki ne da ke jikin gidansu ya yi mata fyade.

Aminiya ta ruwaito marigayiyar ta kuma gane wanda ake zargi tare da nuna shi da ake je ofishin ‘yan sanda.

An garzaya da yarinyar asibiti ne bayan da ciwon da ya ji mata ya tsananta, ana zuwa rai ya yi halinsa. Likitan da ya duba ta ya ce, yarinyar ta rasu ne a sakamakon bugun zuciya da firgici.

Iyayen yarinyar sun yi kira da a bi musu kadin ‘yarsu ta hanyar hukunta wanda ake zargi.

Sai dai kakakin rundunar yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bai samu tabbaci kan faruwar lamarin ba.