Iyalan marigayi Douglas Osunde a birnin Benin na Jihar Edo sun miƙa kokensu ga Rundunar ’Yan sandan Jihar kan ta bi musu kadin mutuwar ɗansu ba zato ba tsammani, a hannun wata mai sana’ar gini a jihar.
Douglas Osunde ya rasu ne yayin da yake aiki da matar mai suna Blessing Uwadiae a matsayin brikila mai koyon gini a garin Benin.
- ’Yan PDP ’yan Arewa sun ziyarci Shugaban Jam’iyyar na Edo
- Hausawa sun nemi gwamnatin Oyo ta gina musu rijiyar burtsatse a Garejin Akinyele
Iyalan sun kuma musanta harin da aka ce an kai wa ’yan uwan Uwadiae na Ugo Niyekhoronmwon a Ƙaramar Hukumar Orhionmwon da wasu waɗanda ba a san ko su wane ne suka kai wa iyalan matar kan rasuwar Douglas ba.
Mahaifin marigayin, Tony Osunde, ya zargi maginiyar da yin sakaci a aikinta wanda a cewarsa, hakan ya kai ga wani ginshiƙin gini ya faɗa a kan ɗan nasa.
“Ni ne mahaifin marigayi Douglas wanda mai koyon aiki ne a wurin Blessing Uwadiae mai sana’ar gini a Benin City.
“Gaskiya ɗana ya rasu, kuma a cewar shugabar tasa ya rasu ne yayin da suke aiki, sai ɗaya daga cikin ginshiƙan ginin ya faɗo a kan Douglas, wanda hakan ya sa aka kai shi asibiti daga bisani ya rasu,” in ji shi.
A baya dai iyalan Uwadiae sun yi zargin cewa a duk lokacin da ’yan uwansu suka ziyarci birnin Benin sai sun fuskanci hare-hare na ɗaukar fansa daga wasu mutanen da suke kyautata zaton dangin Osunde ne saboda rasuwar Douglas.
Da yake magana da manema labarai a garin Benin, wani ɗan gidan, Uwadiae, mai suna Edorodion, ya ce an sake kai wa iyalansa hari kwanan nan.
Ya yi zargin cewa wani ƙanensa mai suna Mista Osadebamwen, ya samu munanan raunuka sakamakon harin wasu ’yan bindiga da ake zargin daga dangin waɗanda ake zargin suka fito.
Sai dai da yake mayar da martani kan zarge-zargen, Tony Osunde ya ce duk da zargin da suke yi wa Blessing na alhakin rasuwar ɗansu, ba su taɓa kai mata ko ’yan uwanta harin ramuwar gayya ko ɗaukar fansa ba kan rasuwarsa.
Ya ce, bayan tabbatar da rasuwar ɗan nasa, nan take ya sanar da ’yan sanda lamarin.
Ya ce ya fara zargin wasa ne lokacin da uwar ɗakin ɗan nasa, wadda ya ce ta ce ta je banki ne domin samun kuɗin magani, amma ba ta koma asibiti ba bayan da aka tabbatar da cewa ɗansa ya rasu.