✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyaye sun yi yunkurin tsafi da ’yarsu a Jihar Ogun

Dubun wasu iyaye ta cika bayan da suka yi yunƙurin yin tsafi da ’yarsu ’yar shekaru bakwai, inda suka guntule mata yatsunta na hannun dama…

Dubun wasu iyaye ta cika bayan da suka yi yunƙurin yin tsafi da ’yarsu ’yar shekaru bakwai, inda suka guntule mata yatsunta na hannun dama kuma suka ɗaure ta, suka sanya ta cikin buhu, sannan suka jefar da ita a bakin mararrabar hanya.

A cewar kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun, ASP Abimbola Oyeyemi, mutanen yankin Asabala da ke kan hanyar zuwa garin Shagamu ne suka yi tozali da wani baƙon abu a farin buhun shinkafa, wanda aka aje a gefen hanya, abun da ba su saba ganin irinsa ba, suka kuma nuna rashin yardarsu da shi. Nan suka ankarar da rundunar ’yan sandan yankin, inda kuma nan take DPO na Owode Egba CSP Shehu Ala ya jagoranci tawagarsa zuwa wajan.

Bayan sun kwance farin buhun sai suka yi kiciɓis da yarinya ’yar shekara 7 mai suna Abibat Adeyemo, wacce aka yanke wa ɗan yatsan hannunta na dama tun ranar juma’ar da ta gabata, inda ta yi kwana daya a cikin buhun.  Bayan da jami’an ’yan sandan suka lura cewa da sauran numfashinta ne, sai suka garzaya da ita zuwa asibiti. A lokacin da ta farfaɗo ne ta shaida cewa mahaifinta ne tare da kishiyar uwarta suka yanke mata ɗan yatsa kana suka ɗaure ta suka sanya ta a buhu, inda suka jefar da ita a gefen hanya. “Daga nan ne muka tura jami’anmu, inda suka yi nasarar kame mahaifin yarinyar mai suna Nasiru Adeyemo da matarsa Idayat Adeyemo a ranar Lahadin da ta gabata,” injii kakakin.

Tuni dai Kwamishinan ’yan sanda a jihar, Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin a kai waɗanda ake zargi zuwa sashin rundunar na musamman da ke binciken ayyukan masu yin garkuwa da yin tsafi da mutane domin zurfafa bincike kafin daga bisani a kai su kotu.