Wadansu ma’aurata masu suna Chinonso Anyanwu da matarsa Oluebube Anyawu, sun sayar da jarirnsu namiji tilo a kan Naira dubu 300. Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa ma’auratan da suka sayar da jaririn dansu suna da ’ya’ya biyu. Wannan al’amari ba karamin mamaki ya bai wa al’ummar karkararsu ba, ganin cewa, dansu namiji ke nan da suka samu ana murna amma sai ga shi sun sayar da shi.
Wannan lamari ya faru ne a garin Umuezike a yankin Amorka da ke Karamar Hukumar Ihiala, Jihar Anambra.
Aminiya ta samu labarin cewa ma’auratan wadanda ’yan asalin Jihar Imo ne mazauna Anambra sun sayar wa wata mace mai suna Sandra Odumege da jaririn dan kwana uku ne kan Naira dubu 300.
Lokacin da suke hannun ’yan sanda ba su yi wani bayani kan dalilan da ya sanya suka kai ga sayar da jaririn nasu ba.
Idan za a iya tunawa makon jiya ma wani magidanci a Jihar Kuros Riba ya kai ’ya’yansa biyu tagwaye ga wadansu don sayarwa.
Kwamishinan ’Yan sandan jihar Anambra Alhaji Haruna Muhammed ya tabbatar wa Aminiya da aukuwar wannan lamari inda ya ce, bayanan sirri da suka samu daga jami’ansu ne ya sanya suka yi nasarar kama mata da mijin da kuma Sandra Odimege da ta sayi jaririn.
Ya ce jami’ansu da ke yankin Ihiala ne suka kama wadanda ake zargin tare da kubutar da jaririn lafiya.
Kwamishinan ’Yan sandan ya ce, nan gaba kadan idan suka kammala bincike za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.