✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

 Iyaye ku daina boye Cin Zarafin da aka yi wa ‘ya‘yan ku —FIDA

IDA tana bin bahasin wadanda aka ci zarafinsu musamman mata da kananan yara.

Kungiyar Lauyoyi Mata ta Duniya (FIDA) reshen Zariya, ta yi kira ga iyayen da su daina boye cin zarfin da ka yi wa ’ya’yan su don gudun tsangwama daga al’umma.

Kungiyar ta yi wannan kira ne ta bakin Dokta Lateefat Bello a wani jawabi da ta gabatar a Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, a yayin da ta kai masa ziyarar ban girma.

Kungiyar ta kai ziyarar ce bayan wani tattaki da ta gudanar daga Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke Sabon Gari zuwa Fadar Sarkin Zazzau don fadakar da al’umma kan manufofi da kuma alfanunta.

Tattakin na daga cikin jerin bukukuwan bikin Makon Lauyoyi Mata ta Duniya wadda za a kammala a ranar Asabar 22 ga watan Oktoba

Shugabar ta ce kungiyar tana neman tallafi daga masarauta a kokarinta na kafa wata gidauniya don tallafa wa wadanda aka ci zarafinsu.

Shugabar ta ce Kungiyar FIDA tana bin bahasin wadanda aka ci zarafinsu musamman mata da kananan yara.