Iyaye da dalibai a Jihar Kaduna sun nuna rashin jin dadinsu kan matakin gwamnatin jihar ta dauka na kin bude makarantu a ranar Litinin, 18 ga watan Janairu duba da yadda mafi akasarin jihohi suka bude nasu makarantun.
Wani mahaifi a Jihar Kaduna mai suna Salisu Suleiman ya ce, “Gaskiya a zuciya ta banji dadin rashin bude makarantu ba tunda sauran jihohi sun bude nasu.”
- Gwamnati ta rushe gidajen masu garkuwa da mutane a Kuros Riba
- An kubutar da ’yan Kasar Nijar 9 daga hannun masu garkuwa a Jihar Katsina
- Jonathan zai jagoranci taron Daily Trust ranar Alhamis
“Amma muna nan muna zuba ido mu ga yaushe za a bude domin yaranmu su koma makarantu mu kuma iyaye a faranta mana rai.”
Wata mata Halima Abullahi wacce uwa ce ita ma ta ce, “Karatun yara na ci gaba da samun koma baya domin su kansu yaran ba dadi suke ji ba zaman gidan da suke yi.”
Ta ce, “wannan dogon zama da suke yi a gida zai shafi jadawalin tsarin karatunsu a duk sanda aka bude makarantun kuma wannan ya sa mu kanmu iyaye ba mu jin dadin zaman gidan da suke yi sannan kuma ga shi karatu ta yanar gizo da aka ce su yi bai da wani tasiri sosai,” inji ta.
Shi kuwa Malam Aliyu Suleiman wanda magidanci ne ya ce, “Ban ji dadi ba kasancewar yaran sun dade a gida babu karatun addini ballantana na zamani kuma ga shi iyaye ba su iya koyar da yaran a gida.”
“Saboda haka, idan har ba a dauki mataki ba gaskiya ilmin yara zai tabarbare a Arewa,” inji shi.
Ali Abubakar, wanda dalibi ne a Jami’ar Jihar Kaduna shi kuwa cewa ya yi, “Rashin komawa makaranta a kullum sake sa mu cikin damuwa yake yi tunda su manyan mutane da masu kudi ’ya’yansu na kasashen waje suna karatu amma mu ’ya’yan talakawa da ke a Najeriya kuma sai mayar da mu baya ake yi ta hanyar kin bude mana makarantu domin mu ci gaba da karatuttukanmu” inji shi.