Babban dan takarar kujerar sarautar Zazzau, Alhaji Bashar Aminu ya garzaya kotu neman ta ayyana shi a matsayin halastaccen Sarkin Zazzau na 19 tare da soke nadin Sarki Ahmed Nuhu Bamalli.
Bashar Aminu wanda shi ne Iyan Zazzau na bukatar kotun ta ayyana nadin da aka yi wa Ahmed Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau da cewa “haramtacce ne wanda aka yi gaban kai a ciki”.
- Iyan Zazzau ya kai El-Rufai kotu kan nadin Sarki
- Tirka-tirkar da aka yi kan nada Sarkin Zazzau
- Sarkin Zazzau: Masu Zaben Sarki sun yi mubaya’a
“Ba shi da halasci da tasiri kuma ya saba ka’ida da dokar kasa, babu adalci a cikinsa sannan ya saba wa lafiyayyen tunani”, inji akardar karar da ya shigar a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna.
Yana kuma neman kotun ta hana Gwamnan Jihar Kaduna, Antoni-Janar na jihar, Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna da kuma Majalisar Masarautar Zazzau yi wa Ambasada Bamalli nadi ko ba shi sandar mulki har sai an kammala shari’ar.
Iyan Zazzau wanda ya fito daga gidan Katsinawa shi ne ya fi samun yawan kuri’u a zaben da masu zabar sarki yi ranar 24 ga watan Satumba, 2020, inda ya samu kuri’a 89.
Takardar karar na neman kotun ta ayyana shi a matsayin halastaccen Sarki Zazzau bisa zaben da Majalisar Zabar Sarkin Zazzau suka gunadar a Fadar Sarkin Zazzau.
“Mai karar wanda Majalisar Zabar Sarki ta zaba na da hakki Gwamnan Jihar Kaduna ya nada shi Sarkin Zazzau bisa tanadin Sashe na 3 na Sabuwar dokar (Nadawa da Tube) Sarakuna na Jihar Kaduna ta 1991.
“Bayan ya samu kuri’u mafiya yawa a zaben da masu zabar sarki suka yi, mai shigar da karar ya samu halascin hawa kujerar mulkin Sarkin Zazzau tun daga ranar da aka yi zaben”.
Mutum 10 da Iyan Zazzau ya maka a kotu su ne Gwamnan Jihar Kaduna, Antoni-Janar Na jihar, Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna da kuma Majalisar Masarautar Zazzau.
Sauran mutum biyar din su ne Wazirin Zazzau, Fagachin Zazzau, Makama Karamin Zazzau, Limamin Juma’an Zazzau, Limamin Konan Zazzau, da kuma Sabon Sarkin Zazzau da aka nada.
Ana iya tunawa Alhaji Bashar Aminu na daga cikin mutum uku da suka fi samun tagomashi daga cikin ’yan takarar kujerar ta Sarkin Zazzau a zaben da masu zaben sarki suka gudanar.
Yayin da ya samu maki kuri’a 89, Yariman Zazzau Alhaji Muhammad Munir Ja’afaru daga gidan Barebari ya zo na biyu da kuri’a 87 sai kuma Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris daga gidan Katsinawa a matsayi na uku da guda53.