✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyalan ’yan sanda da suka rasu sun karbin cekin kudi N80m a Gombe

An biya iyalan yan sanda da suka rasu a bakin Jihar Gombe hakkokinsu inda suka karbi cekin kudi Naira miliyan 80

Iyalan ’yan sanda 19 da suka rasu a bakin Jihar Gombe sun karbi cekin kudi Naira miliyan 80 a matsayin hakkokinsu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hayatu Usman, ya jinjina wa ’yan sandan da suka kwanta dama.

Ya ce ba za a taba manta gudummawarsu ba da kuma yadda suka sadaukar da rayuwarsu ga kasarsu.

Kwamishinan ya yi addu’ar samun rahama, ya kuma bakaci iyalan su ci gaba da yi musu addu’a a kodayaushe.

Da yake mika wa iyalan cekin kudaden a hedikwatar rundumar, CP Hayatu ya shawarce su da su ririta abin da suka samu.

Kwamishinan ya mika wa iyalan cakin kudin ne a madadin shugaban ’yan sandan Najeriya, a karkashin shirinsa na kula da iyalan ’yan sanda.

Wakiliyar iyalan mamatan ta yi godiya ga rundunar bisa yadda ta biya su hakkokin mazajensu da ’yan uwansu domin rage musu wahalhalun rayuwa.