✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyalan Dan Majalisar da aka kashe sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga

Mata biyu da diyar marigayi Musa Mante Baraza, Dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi da aka kashe a makon da ya gabata, sun kubuta daga hannun…

Mata biyu da diyar marigayi Musa Mante Baraza, Dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi da aka kashe a makon da ya gabata, sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, DSP Ahmed Mohammed Wakili, shi ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da wakilanmu ta wayar tarho.

DSP Wakil ya ce da misalin karfe 11.00 na daren Litinin ne tawagar jami’an ‘yan sanda ta ceto iyalan Marigayi Baraza daga hannun ‘yan ta’adda ba tare da biyan ko asi na kudin fansa ba.

Babban jami’in dan sandan ya bayyana cewa, ba tare da jinkiri ba, an kuma garzaya da iyalan dan majalisar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa domin bincikar lafiyarsu.

Ana iya tuna cewa, a Juma’ar da ta gabata wasu ‘yan bindiga suka kai hari, inda suka kashe dan majalisar mai wakilcin Karamar Hukumar Dass a gidansa, kuma suka yi awon gaba da matasan biyu da kuma jaririya ta goye.