✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Iwobi ba zai buga wasan Najeriya da Kamaru ba

Shahararren dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga wa kulob din Arsenal na Ingila kwallo Aled Iwobi rahotannin sun tabbatar ba zai buga wasan…

Shahararren dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga wa kulob din Arsenal na Ingila kwallo Aled Iwobi rahotannin sun tabbatar ba zai buga wasan da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta yi da Kamaru a yau Juma’a a garin Uyo ba.

Haka kuma dan kwallon ba zai buga wasa karo na biyu da kungiyar za ta yi da Kamaru a ranar Litinin a can kasar Kamaru din ba.

 

dan kwallon dai ya samu wannan koma-baya ne bayan ya ji rauni a lokacin da yake yi wa kulob din Arsenal kwallo a wasan da suka yi da kulob din Liberpool a gasar rukunin firimiyar Ingila a ranar Lahadin da ta wuce inda Liberpool ta lallasa Liberpool da ci 4-0.

Sai dai Iwobi dan shekara 21 ya nuna takaicin yadda ba zai buga wadannan wasanni biyu masu zafi da Kamaru ba. Ya nemi takwarorinsa a kungiyar Super Eagles da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun doke Kamaru don su samu damar hayewa gasar cin kofin duniya a badi a kasar Rasaha.

Tuni kocin Eagles Gernot Rohr ya gayyaci dan kwallon CSKA Mosko da ke Rasha Aaron Samuel don ya maye gurbin Iwobi.

Aaron Samuel dai ya taba buga wa kungiyar Super Eagles kwallo a karkashin horarwar tsohon koci Marigayi Stephen Keshi inda wasan da ya yi wa kungiyar na karshe shi ne a watan Oktoban 2014.