Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar Italiya ta fara bincike a kan zargin nuna wariyar launin fata ga mai tsaron bayan Napoli, Kalidou Koulibaly.
Hukumar tana zargin magoya bayan Kungiyar Kwallon Kafa ta Fiorentina da wannan laifi yayin wasan kungiyoyin biyu a ranar Lahadin makon jiya a gasar Serie A.
- Salah na dab da karya tarihin da Didier Drogba ya kafa
- An nada Farfesa Saleh Pakistan Shugaban Majalisar Malaman Kano
Baya ga Koulibaly ’yan wasan Napoli irin su Bictor Osimhen da Frank Zambo dukkansu sun fuskanci kalaman wariyar da magoya bayan Fiorentina suka rika rerawa a wake bayan Napoli ta lashe wasan da ci 2 – 1.
Kwamitin da Hukumar Kwallon Kafa ta Italiya ta kafa zai je Fiorentina don fara bincike kan batun baya ga faya-fayen bidiyo da kwamitin zai yi amfani da su don tabbatar da zargin.
Baya ga hukumar, ofishin babban mai shigar da kara na Italiya ya fara bincike a kan batun, matakin da yake zuwa bayan tsanantar wariya da ’yan wasa bakar fata suke fuskanta a Nahiyar Turai duk da ikirarin hukumomi na magance matsalar.
Dan wasan dan kasar Senegal ya yi matukar fusata da abin da magoya bayan Forentina suka yi masa har ta kai ga ya shigar da kara, inda ya bukaci a zartar da hukuncin dakatarwar har abada ga duk wanda aka samu da laifin rera masa wakar na nuna wariya.
Wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram ya bayyana yadda magoya bayan suke kiransa da dan biri a duk lokacin da ya dauki kwallo, inda ya ce irin wadannan mutane sam ba su cancanci ci gaba da kasancewa a filin wasa ba.