✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta yi jana’izar mayakanta da sojoji suka kashe a Borno

Dakarun sojin saman Najeriya sun yi musu luguden wuta.

Kungiyar ’yan ta’adda ta ISWAP ta gudanar da jana’izar wasu dakarunta da sojojin saman Najeriya suka kashe  a ranar 19 ga watan Maris a Karamar Hukumar Mafa a wani kazamin hari da suka kai kan. 

Rahotanni sun ce sun gudanar jana’izar ce a ranar Lahadi a kauyukan Talwari da Muktari da ke Karamar Hukumar Konduga a Jihar Borno.

Kamar yadda masanin nan kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi Zagazola Makama,  ya bayar da rahoton yadda wasu masu dauke da makamai da ake zargin ‘yan kungiyar ISWAP ne, sun hadu da ajalinsu sakamakon  yunkurin  afkawa garin a manyan motoci da babura a kokarinsu na kai hari kan dakarun sojoji.

Kazalika sun yi kokarin kai hari cibiyar tattara bayanan sirri ta Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a garin da misalin karfe 2 na dare, wanda lamarin ya kai su ga halaka sanadin asirinsu da ya tonu.

Sojojin suka kwato manyan motoci kirar Hilux guda biyu da makamai da dama daga hannun ‘yan ta’addan, yayin da wasu daga cikinsu suka tsere.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Zagazola cewa ‘yan ta’addar sun sha alwashin daukar fansa dangane da wannan kisan da aka yi wa ‘yan uwansu da ba asan adadinsu ba.