Mayakan kungiayr ISWAP sun tare matafiya tare da yin awon gaba da su da bakin bindiga a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a ranar Asabar.
- ‘Ina kallo ’ya’yana 4 da mahaifiyata suka kone kurmus a harin ’yan bindiga’
- Sabon Birni: ’Yan bindiga sun kara kashe mutane bayan ziyarar Tambuwal
Majiyarmu ta tsaro ta ce, “Gaskiya ne an kai wa matafiya hari a safiyar nan a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, inda wadannan mutanen suka yi awon gaba da fasinjojin da ba a san adadinsu ba a tsaksain Benishiek da Mainok; Kawo yanzu dai ba mu da bayanai sosai.”
Majiyar ta ce ce matafiyan na hanyarsu ta zuwa Maiduguri daga Damaturu ne mayakan na ISWAP suka tare su bayan sun wuce Benisheik suka tafi da su zuwa inda ba a sani ba.
Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula a Yankin Arewa maso Gabas, Ambasada Ahmed Shehu, ya tabbatar da wakilinmu da labarin garkuwa da matafiyan.