✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ISWAP ta saki bidiyon kai hari kwalejin Buratai

Rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai a kan harin ba kawo yanzu.

Kungiyar ISWAP mai ikirarin jihadi a Yammacin Afirka, ta fitar da wani bidiyo da hotuna wadanda ta yi ikirarin cewa suna nuna yadda ta kai hari a wata makarantar sojoji da ke Jihar Borno.

Bayanai sun ce makarantar da aka kai harin wata Kwaleji ce da ake kira Tukur Buratai Institute for War and Peace inda ake zargin an kashe fararen hula biyu.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai a kan harin ba kawo yanzu.

ISWAP ta saki bidiyon ne a ranar 13 ga watan Janairu ta manhajar Telegram.

Wata kafar yada labarai ta ISWAP mai suna Amaq ce ta shirya bidiyon, inda a jiki, an yi masa take da “Mayakan ISWAP a yayin da suka kai hari a Kwalejin yaki ta Najeriya da ke garin Buratai a Litinin din da ta gabata.”

A bidiyon, an nuna mayakan a cikin motocin sojoji kirar a-kori-kura wadanda ake kyautata zaton an kwace su ne daga hannun sojoji, inda suka shiga cibiyar sojojin tare da bude wuta ta hanyar amfani da manya da kananan makamai.

Manyan alluna da kuma ginin ya nuna cewa cibiyar ce ta Nazarin Yaki da Zaman Lafiya ta Buratai.

Haka kuma daga baya bidiyon ya nuna mayakan na ISWAP a gaban kofar shiga harabar makarantar amma ba su shiga har cikin kuryar makarantar ba.

An nuna yadda mayakan suka rinka saukar da tutoci da kuma kona su. Haka kuma an nuna su a tsaye a gaban motocin sojoji wadanda suka cinna wa wuta.

Sauran hotunan da aka saka guda takwas sun nuna motocin sojoji wadanda da alamu kungiyar ke son nuna ko ta kwace ko kuma ta lalata su.

BBC ya ruwaito cewa duka hotunan an yi musu take da “Daya daga cikin yadda harin da aka kai a Kwalejin sojoji ta garin Buratai ya kasance.”

Haka kuma wasu hotunan sun nuna yadda motoci suka kone da kuma lalata su, wasu hotunan kuma sun nuna manyan motoci masu sulke wadanda lafiyarsu kalau wadanda ake kyautata zaton mayakan suka tuka su.

A daya daga cikin matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka na yaki da ta’addanci, an bude cibiyar ce a watan Agustan 2020 a garin na Buratai, wanda ya kasance mahaifar tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, wanda ke zaman jakadan Najeriya a Jamhuriyyar Benin.