✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ISWAP ta kwace motocin abincin ’yan gudun hijira a Borno

’Yan ta’addan sun tare ayarin motoci 40 dauke da kayan abincin ’yan gudun hijira

Mayakan kungiyar ISWAP sun tare ayarin wasu motoci 40 dauke da kayan abincin ’yan gudun hijira suka yi awon gaba da wasu daga cikinsu a Jihar Borno.

Kungiyar ta kai harin ne kasa da awa 48 kafin harin farmakin da ta kai a Kurkukun Kuje da ke Abuja, inda ta kubutar da duk mayakanta da ke tsare.

Majiyarmu ta ce maharan na Borno, “Sun kai harin ne a cikin motoci hudu, suka bude wa ayarin motocin abincin wuta suka yi awon gaba da daga cikin motocin suka kwashe kayan abincin da ke cikinsu.”

Majiyar ta ce mayakan kungiyar sun yi awon gaba motocin abincin ne a kauyen  Layi da ke Karamar Hukumar Mobbar ta jihar.

Ta bayyana cewa kayan abincin tallafi ne daga Shirin Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ga ’yan gudun hijira da ke Abadam da kuma mutanen da ke komawa gidajensu a Mobbar.

Majiyarmu ta shaida mana cewa kayan abincin da aka kwace na hanyarsu ta zuwa yankin Damasak ne lokacin da suka fada tarkon  ISWAP.

Aminiya ta samu rahoto cewa yanzu haka kungiyar na yunkurin kwace manyan hanyoyi da wasu muhimman wurare a yankin Arewaci da Kudancin Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun ce tuni ISWAP ta tura motoci hudu dauke da mayakanta zuwa yankin Kareto da ke Mobbar.

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Hamza Idris, Hamisu Kabir Matazu & Muideen Olaniyi

%d bloggers like this: