✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP Ta Kashe Masunta 15 A Borno

’Yan ta'addar sun mamaye yankin ne dauke da makamai, suka tattaro masuntan suka jera su kafin su bude musu wuta.

Mayakan ISWAP sun yi wa  masunta akalla 15 kisan gilla a yankin Tumbun Rogo Kangarwa da ke Karamar Hukumar Kukawa a Jihar Borno.

Wata majiya ta bayyana cewar matakan sun kai harin ne da misalin karfe 11 na dare, a lokacin da masunta ke shirin shiga ruwa da zimmar kamun kifi a ranar Lahadi.

A cewar wata majiya, ’yan ta’addar sun mamaye yankin ne dauke da makamai, suka tattaro masuntan suka jera su kafin su bude musu wuta.

Majiyar ta kara da cewar akalla masunta 15 ne suka mutu, amma wasu da suka tsira da da raunukan harbi suna karbar magani a Kross Kauwa.

Wannan ya kawo adadin hare-haren da aka kai wa masunta a yankin zuwa uku daga watan Fabrairun wannan shekara ta 2024.

Majiyar ta bayyana cewa ’yan ta’addar ISWAP da na Boko Haram sukan kai wa masunta hari idan sojoji suka tare kayan aikinsu, sai su wuce a kan masunta da tunanin su ke kai rahoton su ga sojojin.

A wani harin da aka kai a baya, an kashe masunta tara, kuma ‘yan ta’addan sun yi bincike a kan gawarwakin da aka kashe don neman wasu kayayyaki masu daraja mallakar masuntan.

Wannan tashin hankalin ya jefa al’ummar masu kamun kifi cikin rudani, don haka muna kira ga hukumomin tsaro da su cigaba da  daukar matakin tabbatar da tsaron lafiyar wadannan fararen hula in ji masu ruwa da tsaki na yankin.