Kungiyar ISWAP mai da’awar jihadi a Yammacin Afirka, ta kashe akalla manoma 11 a wani hari da ta kai Kudancin Jihar Borno a ranar Asabar.
Bayanai sun ce mayakan ISWAP sun farmaki yankin mai tazarar kilomita 25 tsakaninsa da birnin Maiduguri inda suka kashe manoman 11 a kauyen Sabon Gari da ke Karamar Hukumar Damboa.
- PDP ta lashe zaben cike gurbi na mazabar Jos ta Arewa da Bassa
- Ukraine ta amince da zaman sasanci da Rasha a Belarus
Wata majiya daga hukumomin tsaro ta ce an tsinto gawarwakin mamata bakwai a ranar Asabar, inda kuma a ranar Lahadi aka tsinto karin wasu hudu.
Majiyar ta ce har da wata mace daya a cikin wadanda lamarin ya shafa.
A makonnin da suka gabata ne mayakan kungiyar ISWAP 104 da suka mika wuya da cewar uwar bari suka gani a sakamakon ragargazar da sojoji ke musu ta sama da kasa.
Karin mayakan kungiyar ta’addancin da suka mika wuya sun bayyana cewa yin hakan ya zame musu dole ne saboda ragarzazar da jiragen yaki da sojojin kasa suke wa maboyarsu.