Mayakan kungiyar ISWAP sun kai sabon hari tare da yin garkuwa da ’yan mata a Karamar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.
Wani rahoto a daren ranar Talata ya nuna mayakan na ISWAP sun kai hari a kauyen Yimirmigza, da kare karamar hukumar inda suka yi garkuwa da wasu ’yan mata uku.
- Hatsarin jirgin sama 11 da suka kashe hafsoshin sojin Najeriya
- ’Yan bindiga sun harbe sabon Kansila sun sace matan aure a Katsina
Aminiya ta samu rahoto cewa bayan sace ’yan matan, maharan suka tuntubi iyalan daya daga cikinsu ta wayar tarho.
Wata tattaunawa da aka nada tsakanin mayakan da dan uwan budurwar, ta nuna cewa mayakan na ISWAP suna da yawan gaske.
Dan uwa budurwar ya tambayi mayakan kan yadda za su taimaka a sako ’yan matan, amma dan bindigar ya ce ba shi da hurumin yin haka sai shugabanninsu sun ba da umarni.
Yayin da take tattaunawa da yaren Chibok, daya daga cikin ’yan matan ta ce ’yan ta’addan sun kai dari a yayin da suka dauke su.
“Wadannan mutanen sun yi yawa matuka kuma a yanzu mu ’yan mata uku ne kawai a hannunsu,” inji ta.