Wasu ’yan ta’addan da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram ɓangaren ISWAP sun tayar da wata na’ura mai fashewa a kan gadar Mandafuma da ke kan hanyar Biu zuwa Damboa da tsakar daren wayewar garin ranar Talata.
Kamar yadda majiyar Zagazola Makama ke cewar, wannan harin na bam da waɗannan ‘yan ta’addan suka jefa ya lalata gadar ta Mandafuna gaba ɗayanta.
- Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba
- ’Yan bindiga sun sace makiyaya 5, da shanu 1,200 a Kaduna
A cewar majiyar, wannan lalacewar gadar a halin da ake ciki ya kai ga katsewar hanyar da ke tsakanin ƙauyen Mandafuma da garin Biu wadda ita ce hanyar da ta haɗa garin Biu da Maiduguri Jihar Borno.
Kamar yadda majiyar ke cewar, wannan aikin ta’addanci an yi shi ne da nufin daƙile zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyar, tare da hana masu ababen hawa da fasinjoji walwala akan wannan hanyar mota.
Har ila yau, wannan ɓarna za ta taimaka wajen hana ƙarfafa ayyukan sojojin da ke kai kawo a cikin wannan yankin don gudanar da harkokin tsaro.