✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP na shirin kaddamar da hari a Zamfara —Gwamnati

Gwamnatin Zamfara ta ce daruruwan mayakan ISWAP na shirin kaddamar da hare-hare a kwanan nan.

Gwamnatin Zamfara ta ce mayakan ISWAP sun fara kafa sansanoni a sassan jihar.

Shugaban Kwamitin Hukunta Laifukan ’Yan Bindiga da Dangoginsu kuma Shugaban Kwamitin Hadin Gwiwa kan Tsaro da Tara Bayanan Sirri na jihar, Sani Abdullahi Shinkafi, ya ce daruruwan mayakan ISWAP sun yi kaka-gida a yankin Mutu da ke karamar Hukumar Mada ta jihar.

A cewarsa, mayakan na shigowa jihar ne ta yankin Danjibga-Kunchin Kalgo da ke Karamar Hukumar Tsafe, kuma suna shirin kai wasu a kauyuka hare-hare a ’yan kwanakin nan.

Ya yi wannan bayani a lokacin da yake karin haske a Gusau, hedikwatar jihar, kan sukar da aka yi wa gwamantin jihar kan matakin da ta dauka na rufe wasu gidajen rediyo da talabijin saboda abin da ta kira dalilan tsaro.

Ya ce, “Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya yi bin da doka ta tanada da ya sanya hannu kan Dokar Gwamna ta 10 da ta ba da damar rufe wasu gidajen rediyo da talabijin a jihar.

“Matakin ya yi daidai da Babi na 2, Sashe na 14, Karamin Sashe ne 2b na kundin tsarin mulkin Najeriya, saboda dalilan tsaro.

“Kundin tsarin muki ya bayyana akin kowanne daga bangarorin zartarwa da na shari’a da kuma bangaren majalisar.

“Shi ya sa aka dauki matakin domin tabbatar da tsaro a jihar, sai dai kuma idan mutum ba dan Najeriya ba ne, ko kuma ya kau da kansa da gangan daga abubuwan da ke faruwa a jihar.

“Gwamnan ya yi haka ne a matsayin matakin tsaro ba wai don hana ’yancin fadin albarkacin baki ba, kamar yadda ake yadawa.

“Tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a abu ne da babu makawa.

“Mun ji abubuawn da kungiyoyi da dama suka fada a kan batun, kamar kungiyar NUJ, NBC, IPI kuma mun fahimce su.

“Amma zargin da kungiyar BON ta yi cewa gwamnan ya nemi muttsike kafofin yada labaran ne, ba gaskiya ba ne, amma duk da haka muna ba da hakuri kan matakin da muka dauka,” inji Dokta Shinkafi.