✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila: ’Yar ta’adda mai lasisi

Hare-haren Isra’ila galibi suna fadawa ne a kan gidajen da suke cike da iyalai a Gaza.

Ga dukkan alamu dai Isra’ila ta zama ’yar ta’adda mai lasisi ko ’yar gatan ’yan ta’addan duniya inda take aikata abin da ta ga dama a kan Faasdinawa Musulmi da Kirista.

Isra’ila tana cin karen ba babbaka ne yayin da manyan kasashen duniya suka zuba mata ido tana ta karkashe yara da tsofaffi da mata fararen hula a gidaje da asibitoci da sansanonin gudun hijira a sassan kasar Faladinu.

In aka dubi abin da ya faru a karshen makon jiya na hallaka mayunwatan da suke kokarin isa ga ’yan lomomin abincin da aka shigar kasar, amma sojojin Isra’ila suka karkashe su, za a ga tsabagen rashin imani da rashin tausayi da rashin mutuntaka.

Wannan mugun ta’addanci da Isra’ila ke aikatawa ga Falasdinawa da sunan yaki da Hamas kuma kasashen Yammacin Turai da kanwa uwar gami Amurka, suka shafa wa fuskokinsu toka, suka toshe kunnuwansu, babban abin takaici ne da ke nuna duniya ta rasa abin da ake kira tausayi da sanin ya kamata.

Kuma ina jin ganin irin tsabagen rashin imanin da sojojin Isra’ila suke aikatawa ne ya sa hatta wasu manyan sanatocin Jam’iyyar Democrat mai mulkin Amurka suka fara kiraye-kirayen lallai ‘A dakatar da kisan da ake yi’ a Gaza kamar yadda kafar labarai ta CNN ta ruwaito a ranar Lahadin da ta gabata.

Kafar CNN ta ruwaito Sanata Dick Durbin na Jihar Illinois kuma Sanata na biyu mafi girma na Jam’iyyar Democrat a Majalisar Dokokin Amurka yana cewa a ranar Lahadin “wajibi ne a dakatar da kashe mutanen” da ba su da laifin komai a Gaza, kuma akwai bukatar Amurka ta mayar da hankali a kan samar da tsarin tsagaita wuta tare da kawo karshen rikicin.

Ya ce, yana sane da ’yancin Isra’ila na rayuwa da ’yancinta na kare kanta kuma abin da ’yan ta’addan Hamas suka aikata a ranar 7 ga Oktoba, mummunan laifi ne abin Allah wadai.

“Amma an kai wani matsayi da aka kashe sama da mutum 25,000 da ba su aikata laifin komai ba da sunan tuttuge Hamas, kuma kullum abubuwan kara lalacewa suke,” Durbin ya shaida wa CNN a shirinta na “Halin da Kasa ke ciki.”

Sanata Durbin ya ce ya amince da kalaman Sanata Chris Murphy na Jihar Connecticut shi ma na Jam’iyyar Democrat da aka buga a jaridar The Washington Post.

“Idan wannan shi ne abin da yakin zai ci gaba da nunawa, ana harbewa da tattake mutanen da suke rububi a kan dan abin da za su toshe uwar hanjinsu a motocin da suke shiga Gaza, to, bai dace Amurka ta ci gaba da kasancewa da wannan bangare ba,” in ji Murphy.

Isra’ila dai kasa ce da ta yi kaurin suna wajen cin zali da keta da danne al’ummar Falasdinawa, a bara kawai Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirori 15 da suke Allah wadai da Isr’ila sakamakon take hakkin Falasdinawa da take yi.

Wannan na nuna ita kadai ta fi sauran kasashen duniya in aka hade su waje guda wajen samun la’anta daga kwamitin.

Haka a shekarar 2015, Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniyar ya amince da kudirori 140 na la’antar Isra’ila a kan yadda take gallaza wa Falasdinawa da makwabtanta da sauran ayyukan da ba su dace ba.

Yayin da in aka tara sauran kasashen duniya sun samu irin wannan suka sau 68 ne.

Daya daga cikin miyagun ayyukan rashin imanin da Isra’ila ta aikata shi ne abin da kafar labarai ta BBC Hausa ta ruwaito a ranar 28 ga Fabrairun da ya gabata na wani Bafalsdine da aka kashe wa dukan ’yan uwansa 103 a Gaza.

Mutumin mai suna Ahmad al-Ghuferi shi kadai ne ya tsira daga harin bam ɗin Isra’ila da ya kawar da iyalansa daga doron kasa.

Harin ya zo ne lokacin da ba ya gidan nasu, yana can maƙale a garin Jericho na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kimanin kilomita 80.

Ahmad na aiki ne a wani wurin da ake aikin gini a Tel Abib, babban birnin Isra’ila, lokacin da Hamas ta kai harin 7 ga Oktoba – ya kasa komawa gida wurin matarsa da ’ya’yansa mata uku sanadiyyar yaƙin da ya ɓarke da kuma rufe hanyar da sojojin Isra’ila suka yi.

A kullum akwai lokacin da suka ware shi da iyalansa domin yin waya da juna idan layin yana da kyau, kuma ko a lokacin da aka kai harin, yana kan waya tare da matarsa Shireen a ranar 8 ga Disamban 2023.

Ranar da sojin Isra’ila suka kashe tad a sauran danginsa ya ce “Kamar ta san cewa za ta mutu, ta ce min in yafe mata kan duk wani abu marar kyau da ta taɓa yi min.

“Na ce mata ta daina irin wannan maganar. Amma wannan ce waya ta ƙarshe a tsakaninmu.”

Wani mummunan harin bam da aka kai a gidan kawunsa a yammacin ranar ce ya hallaka ta da ’ya’yansa mata uku – Tala da Lana da kuma Najla, sai mahaifiyarsa da ’yan uwansa maza huɗu da iyalansu da ’yan uwan mahaifiyarsa da sauran dangi sama da 100.

Wata biyu bayan mummunan harin har yanzu gawarwakin wasu daga cikinsu na ƙarkashin gini.

Wani ɗan uwan Ahmad wanda ya tsira, Hamid al-Ghuferi, ya shaida wa BBC cewa, “Ruwan wuta suka yi ta yi. “An kai hari kan wasu gidaje huɗu da ke kusa da namu, sun dinga jefa bam duk bayan minti 10.”

“Mutum 110 daga iyalan Ghuferi na gidan – yara da ’yan uwa. Duka ban da ƙadan da suka yi saura duk sun mutu.”

Wani kisan rashin imanin da ya auku shi ne na tagwayen jarirai na wata mace mai suna Raina Abu Anza.

Ita dai Raina Abu Anza ta shafe shekara 10 ana yi masa dashen kwayayen jarirai har sau uku don ta samu juna biyu a kokarinta na samun magada.

Sai dai abin bakin ciki ta rasa jariranta masu wata biyar, mace da namiji.

Wani harin Isra’ila ya fada wa gidansu a garin Rafah da ke Kudancin Gaza a cikin dare ranar Asabar da ta gabata, inda ya kashe ’ya’yan nata da mijinta da sauran dangi su 11, yayin da tara kuma suka bace a karkashin buraguzan gini, kamar yadda wadanda suka tsira da jami’an kiwon lafiya na yankin suka tabbatar.

Ta tashi da misalin karfe 10 na dare ta ba jaririnta Na’em nono ta koma barci a gefenta, sai abokiyar tagwaicinsa Wissam a daya gefen, yayin da mijinta ke kwance a kusa da su.

Suna cikin barci bayan awa daya da rabi sai bam ya fada musu gidan ya raushe. “Na yi ihu na yi kuka saboda mutuwar ’ya’yana da mijina,” ta fadi washegari Lahadi da safe lokacin da take shasshekar kuka rungume da gawar jaririyarta.

“Duka sun rasu. Mahaifinsu ya tafi da su ya bar ni,” in ji ta.

Hare-haren Isra’ila galibi suna fadawa ne a kan gidajen da suke cike da iyalai tunda ta fara yaki a Gaza, hatta a birnin Rafah, wadda Isra’ilar ta bayyana da matsera a wata Oktoba, amma yanzu ta dawo tana kai masa miyagun hare-hare ta kasa.

Abin takaici galibin hare-haren na shammata ne ga fararen hula, amma sai ta dora alhakin kisan ta’addancin da ta yi ga Falasdinawan a kan mayakan Hamas cewa su suka jawo hakan.

Daga cikin mutum 14 da aka kashe a gidan Abu Anza, shida kananan yara ne, sai hudu mata, kamar yadda Dokta Marwan Al-Hams, daraktan asibitin da aka kai gawarwaki ya tabbatar.

Farouk Abu Anza, ya ce mazauna gidan su 35 inda wasu aka tarwatsa su daga gidan duka fararen hula ne galibi yara kuma babu dan bindiga a cikinsu.

Rania da mijinta Wissam, masu shekara 29, sun shafe shekara 10 suna neman haihuwa, an yi mata dashen maniyyi sau biyu ba tare da samun nasara ba, ana uku ne ta samu juna biyu inda ta haifi tagwaye a ranar 13 ga Oktoban bara.

Isra’ila ta ci gaba da mummunan yaki da kisan kan mai uwa da wabi, inda ta hallaka Falasdinawa 30,000, kuma ta tilasta kimanin kashi 80 cikin 100 na mazauna Gaza miliyan 2 da dubu 30 barin gidajensu, sannan rubu’in mutanen suna fuskantar matsanaciyar yunwa.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce kananan yara da samari 12,300 Isra’ila ta kashe kuma kaso uku cikin hudu na wadanda aka kashen mata ne da yara.

Shin wadannan kashe-kashe da Isra’ila take yi a Gaza da sauran sassan Falasdinu yaushe za su kawo karshe?

Ko kuwa duniya ta yarje wa Isra’ila ta kawar da Falasdinawa daga bayan kasa ne kacokam?

Shin ba za a samu wasu masu tausayi da tunani su dasa aya aya ga wannan aikin rashin imani ba?