Kasar Isra’ila ta saki Bafalasdinen da ya fi kowane fursuna dadewa a kurkukunta, wato Karim Younis.
An saki Karim mai shekara 66 ne bayan da ya shafe shekara 40 a kurkukun kasar.
- Surukin Ganduje ya kalubalanci hurumin kotun da matarsa ke neman ta raba aurensu
- Mun damka tubabbun ’yan Boko Haram 613 ga jihohinsu na asali – Sojoji
Karim ya fuskanci hukuncin zaman gidan kaso ne sakamakon kashe wani sojan Isra’ila da ya yi a shekarar 1983.
A ranar Alhamis aka sako shi daga kurkukun Hadarim inda ya samu kyakkyawar tarba a wajen jama’ar kauyensu, Ara.
Karim ya shaida wa tashar Aljazeera cewar, sai da aka yawata da shi wurare daban-daban a cikin motocin ‘yan sanda sannan a karshe aka sauke shi a yankin Ranana inda a nan ya samu ya kira ‘yan uwansa da taimakon jama’a.
Bayanai sun ce Karim mutum ne mai muhimmancin ga gwagwarmayar da Falasdiwa ke yin a nema wa kansu ‘yanci.