✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Isra’ila ta kashe Falasdinawa 2 a gabar Kogin Jordan

Isra'ila ta ce wadanda aka kashen suna da hannu a musayar wutar da aka yi a kusa da Gilboa.

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa biyu a wani samame da suka kai ranar Litinin a yammacin gabar Kogin Jordan.

Jami’an Falasdinawa sun ce, sojojin sun ruguza gidajen wasu Falasdinawa biyu da ake zargi da kashe wani sojan Isra’ila.

Ministan Lafiya na kasar ya ce an kashe Falasdinawan ne a wani samame da sojojin Isra’ilar suka kai yankin Jenin.

A cewar sojojin Isra’ila, wadanda aka kashen suna da hannu a musayar wutar da aka yi a kusa da Gilboa (Jalame) wadda ta yi sanadiyar mutuwar Manjo Bar Falah.

Bayanai sun ce al’adar Isra’ila ce rushe gidajen duk wasu da ta yi zargi da hannu a kai wa mutanenta hari.

Sai dai masu rajin kare ’yancin dan Aadam sun ce wannan hali na Isra’ila laifi ne da ka iya haifar da rasa muhalli ga fararen hula ciki har da kananan yara.