Iran na zargin Isra’ila da kai wa jirgin ruwanta hari a Yemen a Bahar Maliya a yayin da ake kokarin cimma yarjejeniyar amfani da Nukiliya da Iran din.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta tabbatar a ranar Laraba cewa jirgin ruwan MV Saviz ya lalace sakamakon harin da aka kai masa a Bahar Maliya ranar Talata.
- ‘Tun ina shekara bakwai mahaifina yake kwanciya da ni’
- An kammala daukar shirin Labarina zango na uku
- Rasha: Putin ya sa hannu kan dokar da zai yi mulki har 2036
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce, “harin ya lalata wani bangare na jirgin ruwan, amma an yi sa’a babu wanda ya samu rauni.”
Tun shekarar 2016 da jirgin ruwan dakon kayan ya fara zarya a tekun da ke kusa da Yemen, ake zargin amfani da shi a matsayin sansanin Sojojin Juyin Juya Hali na Iran (IRGC) da wadata ’yan tawayen Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan Iran da makamai.
MV Saviz ya kuma yi kaurin suna a matsayin cibiyar leken asirin IRGC.
Ana zargin Isra’ila da hannu na kai harin, a yayin da wakilan Iran ke ganawa da Amurka a Vienna domin cimma yarjejeniyar Nukiliya.
Amurka ta ce Isra’ila ce ta kai harin
Gidan talabijin na kasar Iran, ya ambato wani rahoto a jaridar New York Times na kasar Amurka na zargin gwamnatin Isra’ila na sanar da Amurka cewa sojojinnta sun samu jirgin Iran din a ranar Talata.