Fira-Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya sha kaye a zabe bayan shafe shakara 12 a kan karagar mulki.
Ya fara mulki ne tun shekara ta 2009, lamarin da ya sa ya kafa tarihi a matsayin Fira-Minista mafi dadewa a tarihin kasar.
- Shin da gaske baraka ta kunno kai tsakanin Buhari da Tinubu?
- ’Yan bindiga sun hallaka mutum 12 a hanyar Sakkwato zuwa Gusau
Wa’adin mulkinsa ya zo karshe ne ranar Lahadi bayan majalisar kasar ta amince da kafa sabuwar gwamnati wacce jagoran ’yan kishin kasa, Naftali Bennett zai jagoranta.
Mai kimanin shekaru 71 a duniya, Mista Netanyahu wanda ya kasance dan siyasa mafi karfin fada-a-ji a tsakanin takwarorinsa ’yan siyasar Isra’ila, ya sha alwashin dawowa a ci gaba da fafatawa da shi a fagen siyasar na ba da jimawa ba.
A wani yanayi mai cike da hayaniya, magoya bayan jam’iyyar Mista Netanyahu a majalisar sun yi ta ihu suna kiran Naftali a matsayin ‘makaryaci’, sai dai duk da haka sai da ya sha kayi da banbancin kuri’a daya kacal.
Shi dai sabon Fira-Minista Naftali, wanda tsohon Ministan Tsaron kasar ne na da kimanin shekara 49 a duniya kuma hamshakin attajiri ne, ana sa ran zai sha rantsuwar kama mulki nan ba da jimawa ba.
A karkashin yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa dai, Yair Lapid ne zai maye gurbin Naftali a matsayin sabon Fira-Minista a shekarar 2023.
Sabuwar gwamnatin dai wacce aka kafata bayan zaben 23 ga watan Maris din 2021 wanda bai kammala ba, na da kwakkwaran shirin kauracewa batutuwan da suka shafi kasashen ketare, ciki har da na Falasdinu tare da mayar da hankalinta wajen al’amuran cikin gida.
To sai dai Falasdinawan sun ce ko kadan babu abinda sauyin gwamnatin zai canza, suna masu cewa duk kanwar ja ce tsakanin Mista Naftali da Netanyahun.