Wata iska mai karfin gaske tare da mamakon ruwan sama ta yi sanadiyar mutuwar mutum biyu, ta kuma lalata gidaje sama da 1,500 a Kananan Hukumomin Faskari da sabuwa a Jihar Katsina.
Mai magana da yawun hukumar ba da agaji ta Jihar Katsina, Umar Muhammed, ya ce ruwan sama mai karfin gaske da ya shafe sama da sa’a biyar yana kwarara a Karamar Hukumar Bindawa ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu a ranar Litinin 26 ga watan Yuli.
- Yadda matashi ya kashe bazawararsa ya yi wa gawarta fyade
- ‘Da kyar muke numfashi bayan ambaliya ta ritsa da jirginmu’
Ya kara da cewa a garin Bindawa kadai gidaje 400 ne suka salwanta, gidaje sama da 800 kuma a Faskari, sai wasu akalla 300 da aka rasa a Karamar Hukumar Sabuwa.
Umar ya kara da cewa hukumar na -shirye shiryen kai wa al’ummar da lamarin ya shafa dauki.