✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Irin ‘wulakancin’ da masu haihuwa ke fuskanta daga malaman asibiti

Wata matar aure ta ce ta hakura da zuwa asibiti saboda wulakancin malaman asibiti.

Wata matar aure ta ce ta hakura da zuwa asibiti haihuwa saboda wulakancin da ta fuskanta daga malaman asibiti.

Matar mai suna Fatima ta kara da cewa saboda rashin ‘rashin tausayin’ malaman, sai da ta haihu a waje a asibiti.

Fatima ta ce, “Wallahi ba zan sake zuwa assibiti don haihuwa ba,” saboda wulakancin da ta fuskanta daga malaman jinya a lokacin da ta je haihuwa Asibitin Kwararru da ke Murtala Muhammad, Kano.

Fatima ta kara da cewa bayan da ta fara nakuda sai maigidanta ya dauke ta ya kai ta asibitin kwararrun, tun daga shigarsu bangaren masu haihuwa suka fara fuskantar matsala, inda wata ma’aikaciyar jinya ta daka wa maigidan nata tsawa cewa ya daina rike ta, ya bar ta taka da kafafuwanta har dakin haihuwa.

“Matar nan ba ta yi la’akari da halin da nake ciki ba, haka ta fara daka wa ’yan uwana tsawa cewa sai dai su sauke ni in shiga dakin haihuwa da kafata, wanda ni kuma na kasa, saboda ciwon mara da nake yi.

“Ganin na kasa tashi sai ta fara yi min masifa wai kada in sake in haihu a wurin, idan na haihu sai na biya kudin da za a sayi kayan tsafatce wurin. Ni ina ta kaina ma ban saurare ta ba.

“A nan dai suka fara fada da ’yan uwana, ai kuwa ban san lokacin da na haihu a wurin ba.

“Bayan na haihu ne suka kuma dauke ni aka kai ni dakin don yi min abin da ya kamata.”

‘Na kusa rasa ’yata da tagwayenta’

Malama Safiyya Alkassim uwa ce da ta kai ’yarta asibiti don haihuwa.

Ta bayyana wa Aminiya yadda wulakancin ma’ikatan jinya ya kusa janyo mutuwar jikokinta ’yan biyu da ’yarta Maryama ta haifa.

“Bayan an yi wa ’yata tiyata an cire mata ’yan tagwaye a Asibitin Kwararu na Murtala to sai aka ba mu gado.

“To wai a tsarinsu dole idan gari ya waye sai masu kwana da marasa lafiya su fita daga dakin.

“Da farko saboda na ga halin da ’yata mai jegon take ciki domin tana fama da ciwon ciki sai na ki fita.

“Amma suka takura min cewa dole na fita wai doka ce hakan. Kasancewar ba na son rigima sai na fita.

“Ai kuwa can sai ga wata daga cikin ma’aikatan ta zo tana kira na wai in zo wurin ’yata. Ina shiga na same ta tana ta faman murkususu a kasan dakin da ko tabarma babu.

“Nan na fara tambaya, sai wata mara lafiya da ke kusa da gadonta take ba ni labari cewa ba don Allah Ya sa ta kawo dauki ba to da jariran sun mutu, domin a cewarta lokacin da ’yar tawa take ciwon cikin ba tare da ta sani ba ta danne jariran, da yake a gado daya suke kwance.

“Matar ta ce ganin hakan ya sa ta tashi da sauri ta janye yaran tare da kiran ma’aikatan don su ga abin da ke faruwa. Tun daga wannan rana kuwa na daina fita waje har aka sallame mu.”

‘Kanwata ta haihu a cikin mota’

Binciken Aminiya ya gano cewa irin wannan halayyar ta malaman asibiti ana samun ta har a wasu asibitocin kudi.

Wata mata mai suna Hajiya Rabi Sani ta shaida wa Aminiya yadda kanwarta ta haihu a cikin motar tasi sakamakon kin karbar ta da malaman asibitin suka yi.

“Lokacin da ta fara nakuda sai muka je asibitin haihuwa na unguwarmu, na gwamnati ne shi ma, aka ce babu gado.

“Daga nan muka tafi wani asibitin shi ma haka aka ce babu gado.

“A karshe dai sai muka tafi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda motarmu ta je har kofar dakin

haihuwa. Muka bar ta a mota muka shiga don shaida musu abin da ke tafe da mu.

“Amma suka ki sauraren mu, wai su ba su da gado. Mun fi kusan minti 30 muna rokon su amma suka ki

amincewa.

“Muna cikin tunanin abin yi sai kawai yarinyar nan ta haihu a cikin motar tasin nan. Wallahi sai wasu mata da ke waje, wadanda su ma sun kawo ’yan uwansu ne suka cire mayafansu suka kare yarinyar nan domin a gefen motar take.

“Muka koma muka fada musu abin da ya faru sannan suka zo suka yanke cibiya, suka dauke jaririn, mu kuma da taimakon matan nan da suka yi mata rumfa aka dauke ta aka shiga da ita ciki, inda suka yi mata abin da ya kamata.”

Malama Rabi ta kara da cewa, “bayan wanann wulakancin da suka yi mana sai ga shi wai suna neman a biya su kudin haihuwa.

“Ai kuwa dama mutane da dama sun zuga maigidan mai jegon da kada ya biya ko kwabo. Shi kuma ya ce ba zai biya su kudin da suka nema ba, inda ya ce idan ma zai biya to sai dai ya ba su wani abu daga ciki amma ba duka kudin da suka nema ba.”

‘Yadda na haihu a yashi’

Haka kuma a kwanan nan, an samu faruwar irin wannan lamarin a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda ya janyo wata mata ta haihu a cikin yashi; lamarin da ya sa ’yan uwanta suka lashi takobin daukar matakin shari’a a kan hukumar asibitin, kamar yadda mai haihuwar Malama A’isha Auwalu ta shaida wa Aminiya.

“Lokacin da muka zo asibiti sai suka duba ni, suka ce wai ba haihuwa ba ce. Sai maigidana ya ce to shi gaskiya duba da irin halin da nake ciki ba zai mayar da ni gida ba; zai bar ni a asibitin har sai Allah Ya kawo haihuwar.

“Muna zaune a waje sai na ji cikina ya murda, ai kuwa na tashi da niyyar in shiga cikin dakin da suke domin na fada musu abin da nake ji.

“Ina cikin tafiya, akwai wani yashi da ake aikin wani bangaren na dakin haihuwar, ban san lokacin da na tsuguna a kan yashin ba kuma ai kuwa a nan na haihu.

“Haka nan aka dauko jaririyar duk yashi a jikinta har cikin idanuwanta da kunnenta da bakinta. Hakan ya fusata maigidana ya ce sai ya dauki matakin shari’a a kan asibitinsu.”

‘Akwai baragurbi a cikin ma’aikatan asibiti’

Yawancin matan da Aminiya ta tattauna da su, sun yi kira ga gwamnati da ta sa ido tare da bibiyar ayyukan da malaman asibiti ke yi don gano baragurbi a cikinsu tare da dora su a kan hanyar da ta dace musamman bangaren kyautata mu’amala da marasa lafiya.

Aiki ne yaka mana yawa –Ma ’aikatan Jinya

Hajiya A’isha Akilu ma’aikaciyar lafiya ce a Jihar Kano. Ta yi wa Aminiya Karin haske game da batun, inda ta dora alhakin hakan a kan karancin ma’aikata a sibitoci, wanda ya janyo aiki ya yi wa malaman jinya

yawa.

“Gaskiya ba zan yi miki musu cewa ma’aikatan lafiya suna yin hakan ba, domin mu kanmu a cikinmu mun san akwai wadanda ba su da tausayi da sauransu.

“Sai dai a gefe guda akwai laifin gwamnati a ciki domin ma’aikata sun yi kadan don haka muna yin aikin da ya fi karfinmu, majinyata sun yi yawa.

“Wata rana fa sai ki ga mutum ya karbi haihuwa sama da 20, don haka wasu lokutan dole abubuwa makamancin hakan su rika faruwa, musamman ma idan aka yi rashin sa’a mutanen ba masu fahimta ba ne sai ki ga an zo ana kai ruwa rana.

“Amma idan aka yi sa’a cewa marasa lafiya masu saukin hali ne, ko da ma’aikaciyar jinya ta yi fada to za ki ga sun fahimce ta kuma za su san yadda za su yi su shawo kan al’amura cikin ruwan sanyi.”

Ita ma wata ma’aikaciyar asibiti mai suna Fatima Nura, ta bayyana cewa a wasu lokutan majinyata ko ’yan uwansu su ne ke fusata ma’aikatan har su yi musu abin da bai kamata ba.

“Kin san ba kowa ba ne ya iya mu’amala da mutane. Wasu za su zo waje a rude babu natsuwa kuma ba su san yadda za su samu ma’aikata a wanann lokacin ba.

Don haka duka bangarorin suna da laifi. Mu malaman asibiti mu ji tsoron Allah mu kuma yi hakuri. Sannan su ma a bagaren majinyata su rika takatsantsan da ayyukansu da kuma kalamansu.”