An kashe mutum biyu a garin Yaba na Jihar Ondo, inda masu zanga-zangar EndSARS suka kone muhimman gine-gine ofishin Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na siyasa a garin Akure.
Rahotannin sun ce an kuma cinna wa caji ofis dain garin Okitipupa wuta tare da kai har ikan gidan yarin garin inda ‘yan daba suka saki fursunoni fiye da 50.
Wani dan majalisar jihar ya ambato ‘yan sanda na cewa an harbe daya daga cikin mamatan ne yayin da yake kokarin kutsawa harabar bankin GT aka kuma dauke bindigar da yake rike da ita.
Dan majalisar ta ce mutum na biyu kuma an kashe shi ne a gaban wani wurin cin abinci.
A garin Akure kuma an cinna wuta a kan ofishin yakin neman zaben gwamnan jihar Rotimi Akeredolu.
A garin Okitipupa kuma bayanai sun ce maharan sun saki fiye da fursunoni 50 da ke tsare a gidan yarin garin; suka kuma banka wa caji ofis din garin wuta.
Matasan sun kuma kai hari kan sakatariyar Karamar Hukumar da wani asibiti.
Ofishin hukumar zabe, INEC, shi ma ya gamu da fushin masu tarzomar inda suka lalata shi tare da satar kayayyaki.
Majiyoyi sun ce masu tarzomar sun fara taruwa tun da safiyar Alhamis domin ci gaba da zanga-zangar a Okitipupa amma jami’an tsaro suka yi yunkurin dakatar da su.
Hakan ya harzuka su inda daga bisani suka kai hari caji ofis din sa’annan suka dangana da gidan yarin.