Rahotanni na cewa ƙasar Iran ta fara abin da ta kira martani mafi girma da nasara kan hare-haren Amurka.
Kamfanin Dillancin Labaran Iran na Tasnim, ya ce dakarun juyin juya halin ƙasar sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar da Iraƙi.
- Babu dalilin kai wa Iran farmaki — Putin
- Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha
A halin yanzu ne aka samu labaran jin ƙarar abubuwan fashewar a birnin Doha na Qatar.
Qatar mai arzikin man fetur wadda ke da tazarar kilomita 190 da kudancin Iran, tana ɗauke da sansanin sojin Amurka na Al Udeid mafi girma a yankin na Gulf.
Gwamnatin Qatar din ta yi allah wadai da harin da Iran ta kai kan sansanin sojin saman Amurka da ke al-Udeid.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Majed al-Ansari, ya wallafa a shafinsa X cewa: “Mun ɗauki wannan a matsayin keta haddin Qatar da sararin samaniyarta da dokokin duniya da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.”
Ya ce na’urorin kakkaɓo makamai na ƙasar sun “samu nasarar daƙile hare-haren na makamai masu linzami” kuma tuni aka janye dakarun Amurka daga sansanin tun kafin harin.
Ya ƙara da cewa “an ɗauki duka matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaron lafiyar dakarun a sansanin, ciki har da sojojin Qatar, da dakawarun ƙawance da sauransu.
“Mun tabbatar da cewa babu wanda ya rasa rai ko jikkata a harin.”
Kakakin ya ce Qatar na da damar mayar da matarni “domin rama daidai da abin da aka yi mata.”