✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta rataye tsohon jami’in gwamnatinta saboda zama dan leken asirin Birtaniya

Iran na zarginsa a cin amanarta ta hanyar yin aiki ga abokiyar gabarta

Kasar Iran ta rataye tsohon Mataimakin Minsitan Tsaronta, Alireza Akbar, bisa zarginsa da zama dan leken asirin Birtaniya.

Wata mujallar sashen shari’a ta kasar ya tabbatar a ranar Asabar cewa an rataye shi ne bayan kotu ta same shi da laifin yi wa kasar zagon kasa ta hanyar yi wa wata kasar leken asiri.

Alireza Akbar dai na da shaidar zama dan kasashen biyu.

Mujallar ta kuma ce tun kafin wannan ma, sai da aka yanke masa hukuncin kisa bayan samunsa da yi wa tsarin tsaron kasar na ciki da waje makarkashiya.

“Aikin mai leken asirin na birtaniya a wannan shari’ar ya nuna irin tsananin cin amanarsa, yadda aka amince da shi da kuma yadda ya ci amanar ta hanyar taimaka wa abokan gaba,” in ji mujallar.

Iran ta kuma zargi tsohon jami’in nata da cewa ya karbi horo ne a MI-6, sannan ya karkafa wasu kamfanonin da suke yi wa tsarin tattara bayanan sirrinta zagon kasa.

Ta kuma ce a mabanbantan lokuta, Alireza Akbar, ya sha yin taruka a kasahe daban-daban da suka hada da Austria da Hadaddiyar Daular Larabawa, kuma an ba shi shaidar zama dan Birtaniya ne saboda nuna godiya da ayyukansa na cin amanar kasarsa.

Tuni dai Fira Ministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya bayyana hukuncin na Iran a matsayin “ayyuakn matsorata kuma marasa imani da sam ba sa mutunta hakkin dan Adam.”

Ita ma Amurka ta yi kira ga kasar da ta daina zartar da hukuncin kisa saboda ya zama tsohon yayi.

Marigayin dai ya fara aiki ne da Hukumar Leken Asirin Birtaniya a shekarar 2004, inda ya yi mata aikin shekara biyar kafin daga bisani ya bar kasar.

A shekarar 2009, bayanai sun ce Birtaniyar ta shawarce shi da ya bar Iran.

Sai dai bayan shekaru masu yawa, ya sake komawa Iran din domin ci gaba da aikinsa, inda kasar ta cafke shi.

Kodayake ba a bayyana ranar da aka kama shin ba, amma iran ta ce an kai shi gidan kurkuku ne a shekarar 2019.