kasar Iran ta kashe wani masanin Nukiliyarta wanda ta ce ta samu da laifin mika wa kasar Amurka wasu bayanan sirri kan Nukiliyar kasar. An kashe malamin mai suna Shahram Amiri ta hanyar ratayewa.
Amiri dai shi ne wanda aka rika bayar da rahoton an sace shi a kasar Saudiyya a shekarar 2009, bayan da ya bace a watan Mayu ko Yunin 2009, kuma a watan Yunin 2010 ne ya bayyana a kasar Amurka, inda ya ce an sace shi zuwa can ne inda Hukumar Leken Asiri ta Amurka ta yi masa tambayoyi. Sannan a ranar 13 ga watan Yulin 2010, ya bayyana a sashin al’amuran Iran na ofishin Jakadancin Pakistan da ke birnin Washington na Amurka inda ya ce yana son komawa gida Iran.
Ya dawo kasar Iran a kashin kansa a shekarar 2010, inda a watan Mayun 2011 aka kama shi aka yanke masa hukuncin daurin shekaru kan cin amanar kasar. Kuma kwatsam ranar Asabar da ta gabata sai aka samu labarin an rataye shi, bayan da aka mika gawarsa ga mahaifiyarsa wadda ta bayyana cewa akwai alamun daurin igiya a jikin wuyansa.
A ranar Lahadi Kakakin Sashin Shari’a na Iran, Gholamhossein Mohseni Ejei, ya shaida wa manema labarai cewa: “Ta hanyar alkarsa da Amurka, Amiri ya bayar da muhimman bayanan kasar ga makiya.”
Amiri, wanda aka haife shi a 1977, ya bace ne lokacin da ya tafi aikin Hajji a Makka, kuma bayan bayyanarsa a Amurka, ya ce an sace shi ne aka yi ta ‘musguna masa domin ya bayar da wasu bayanan sirri.’
Sai dai jami’an Amurka sun fadi a lokacin cewa Amiri ya gudu Amurka ne a kashin kansa kuma ya ‘bayar da muhimman bayanan.’
Iran ta kashe masanin Nukiliyarta
kasar Iran ta kashe wani masanin Nukiliyarta wanda ta ce ta samu da laifin mika wa kasar Amurka wasu bayanan sirri kan Nukiliyar kasar. An…