✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta daure ’yar tsohon shugaban kasarta

An yanke wa ’yar tsohon shugaban kasar hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari.

Gwamnatin Iran ta daure Faezeh Hashemi, ’yar tsohon shugaban kasar, Akbar Hashemi Rafsanjani, kan yada farfaganda game da sha’anin tsaron kasar.

Lauyanta Neda Shams, ya shaida wa AFP cewa kotu ta yanke mata hukuncin daurin shekara biyar, amma za su daukaka kara.

An kama Faezeh Hashemi a babban birnin kasar, Tehran a ranar 27 ga watan Satumba, 2022 kan zargin tunzura masu zanga-zanga.

Iran na zargin Faezeh mai shekara 60 a duniya da haddasa zanga-zanga tare da hada taron mutane ba bisa ka’ida ba wanda ya tayar da tarzoma da barazanar tsaro a kasar.

A 2012 a gurfanar da ita a kotu kan irin wannan laifi, aka yanke mata hukuncin daurin wata shida a gidan yari.

Hukumomin Iran sun ce an cafke mutane da dama tare da gurfanar da wasu da take za zargi da hannu a zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma a kasar.

Mahaifin Hashemi, wanda ya mulki kasar daga 1989 zuwa 1997, ya rasu a shekarar 2017.