Kwamitin Zartarwa na Majalisar Dinkin Duniya ya sake gudanar da wani taron gaggawa don yi wa Iran hannunka mai sanda kan gwaje-gwajen makaman nukiliya masu linzami masu cin dogon zango da kasar ta yi a baya-baya nan.
A taron sirri da aka gudanar sakamakon bukatar da kasashen Birtaniya da Faransa suka nuna, an kira Amurka ta yi Allah wadai da gwaje-gwajen manyan makaman nukiliya da aka tabbatar da cewa Iran ce ta yi.
Tuni Iran ta mayar da martani, inda ta musanta batun, ta ce nema ake a shafa ma ta bakin fenti babu gaira babu dalili.
Kafar labarai ta TRT ta ruwaito wakiliyar Amurka a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley tana nuna rashin jin dadinta tare da tabbatar da cewa gwamnatin Iran ta take dokokin kasa da kasa kan makaman nukiliya, sannan ta fitar da wata rubutacciyar sanarwa cewa, “Gwaje-gwajen makaman nukiliya da Iran ta yi a baya-bayan nan abu ne mai matukar tayar da hankali. Allah wadai da wannan tsokanar fada da gwamnatin Iran ke yi.”
Haley ta kira Iran da babbar murya da ta bi doka mai lamba 2231 ta Kwamnitin Zartarwar Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya samar da nufin mara wa matakin Shugaban Amurka Donald Trump baya na janyewa daga yarjejeniyar nukiliyar da ta kulla da Iran a shekarar 2015 da kuma gaggauta dakatar da gwaje-gwajen makaman nukiliyar.
Wakilin Birtaniya a Majalisar Dinkin Duniya, Karen Pierce kuma cewa ya yi wadannan tsokane-tsokanen na Iran sun yi hannun riga da matakan Kwamitin Zartarawar.
Jakadan kasar Faransa, François Delattre ma ta goya wa Birtaniya baya, inda ta ce kamata ya yi Iran ta gaggauta dakatar da gwaje-gwajen da a yanzu haka take ci gaba da yi.
Amma shuagabannin kasar Iran sun sanar da cewa, batun gwaje-gwaje makaman nukiliya da ake cewa sun yi zuki ta-malle ce kuma ayyukan da suke ci gaba da gudanarwa a yanzu haka ba su taka dokokin Kwamitin Zartarwa na Majalisar Dinkin Duniya ba.
A nasa bangaren, Ministan Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo kuma cewa ya yi, “Ko shakka babu Iran na ci gaba da gwaje-gwajen makaman iri daban-daban wadanda a ciki akwai na nukiliya da kuma masu cin dogon zango. Wadannan makaman na iya cimma wani shashe na nahiyar Turai da kuma kowane bangare na yankin Gabas ta Tsakiya. Gwada ire-iren wadannan makamai babban laifi ne duba da dokokin Kwamitin Zartarawa na Majalisar Dinkin Duniya, musamman ma doka mai lamba 2231. Shi ya sa muke kiran gwamnatin Iran da ta gaggauta kawo karshen illahirin ayyukanta na gwada ko kuma yin amfani da wadannan makaman.”