Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) game da mastalolinsu da bangarorin ke ta kullin kurciya a kai.
Kakakin Ma’aikatar Kwadago da Samar da Ayyuka, Charles Akpan ya sanar da haka a cikin wani sako, sai dai bai bayyana batutuwan da zaman zai tattauna ba.
- IPPIS: ASUU ta shiga ganawar sirri da jagororin Majalisar Dattawa
- Matsalar tsaro: Kungiyoyin Arewa sun shirya zanga-zanga
“Minista Chris Ngige zai yi zama da Kungiyar Malaman Jami’o’i ranar Alhamis 15 ga Oktoba, 2020”, inji sanarwar.
Wata majiya ta ce zaman zai tattauna da kan tsarin biyan albashin bai-daya na IPPIS da gwamnati ta ce wajibi ne malaman su shiga su kuma suka ce allambaran.
A ranar Talata, washegarin ganawar ASUU da Majalisar Tarayya, gwamanti ta ce tana duba yiwuwar rungumar tsarin biyan albashi na UTAS da kungiyar ta gabatar.
Karin bayani na tafe….