A halin yanzu, Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ta ASUU, ta shiga bayan labule tare da Jagororin Majalisar Dattawa.
ASUU da Shugabannin Majalisar na ganawa a kan rashin jituwar da ke tsakaninta da Gwamnatin Tarayya musamman dangane da tsarin biyan albashi na bai daya (IPPIS).
- WTO: Buhari na ganawar sirri da Okonjo-Iweala
- Yadda malaman jami’a suka yi sabani da ASUU
- Dalilin da ya sa jami’o’i masu zaman kansu ke neman a bude makarantu –ASUU
Gabanin kebancewar da suka yi inda aka nemi manema labarai su janye jiki, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana damuwarsa a kan yadda har kawo yanzu aka gaza cimma matsaya tsakanin Kungiyar Malaman da kuma Gwamnatin Tarayya.
Sanata Lawan yayin bayyana damuwa dangane da rashin cika alkawalin da Gwamnatin Tarayya ta rika yi wa Kungiyar ASUU a baya ya ce, “ina dalilin da za ku kulla yarjejeniyar da kun san ba ku da ikon cika wa?”
Shugaban ASUU Farfesa Biodun Ogunyemi wanda ya jagoranci tawagar kusoshin kungiyar, ya ce ganawar ta su za ta mayar da hankali wajen neman goyon bayan Majalisar Dattawa don tayi ruwa da tsaki wajen ganin Gwamnatin Tarayya ta amince da tsarin biyan albashin da suka kawo sabanin na IPPIS tun tsawon shekaru biyar da suka gabata.
Yayin gabatar da kasafin kudin badi ranar Alhamis a zauren Majalisar Dokoki ta Tarayya, Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar cewa duk Ma’aikacin Gwamnatin Tarayya da bai shigar da bayanansa ba a tsarin IPPIS, ba zai sake samun albashi ba daga yanzu zuwa watan Nuwamba.