Kayan abinci sun yi tashin gwauron zabo a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya bayan ’yan kasuwar Arewa sun dakatar da kai musu kaya saboda kisan gilla da ’yan ta’addan kungiyar IPOB ke wa ’yan arewa a can.
An samu tashin gwauron zabon kayan abincin ne kasa da sa’a 24 bayan yajin aikin shigar da kaya yankin da kungiyar ’yan kasuwar Arewa ta fara a ranar Alhamis saboda kashe ’yan Arewa a yankin Kudu maso Gabas.
- Badakalar N10bn: Kotu ta tura dan uwan Gwamnan Kogi kurkuku
- An kashe ’yan IPOB, an gano masana’antar bom dinsu
Shugaban kungiyar, Auwal Abdullahi Aliyu, ya ce, a kasa da mako guda an kashe ’yan Arewa akalla 100 a yankin Kudu maso Gabas, don haka yajin aikin gargadi na kwana uku da suka shiga ya zama dole, kuma ya fara yin tasirin da suke bukata.
Ya ce, “Mun tare duk manyan hanyoyin shigar da kaya yankin ta jihohin Binuwai, Nasarawa, Kwara da Filato da sauransu, kuma direbobin manyan motocin suna ba mu hadin kai.”
A cewarsa, an dauki matakin ne domin hana matasan Arewa daukar doka a hannunsu da ramuwar gayya, kuma kungiyar ta sanar da shugabannin Arewa game da matakin da ta dauka.
Rahotanni sun nuna yadda a ’yan bindiga suka kashe mutum 24 da sunan aiwatar da umarnin zama a gida dole da IPOB ta kakaba a yankin.
Ana mana dauki-dai-dai
Kakakin kungiyar cigaban ’yan Arewa a jihohi 17 na yankin Kudu, Badamamasi Muhammad, ya ce tashin hankalin da ’yan Arewa suke gani a Kudu maso Gabas ya sa sun fara kaura zuwa Arewa.
A cewarsa, ’yan kalilan da suka rage a manyan garuruwan yankin suna cikin zullumi, kuma yawancin wadanda suka ci gaba da zama a Kudu maso Gabas ba su da wani zabi.
Ya ce, “Yawancinmu a nan aka haife mu, a nan muka taso, kuma nan ne garinmu.
“Wasu sun gwammace zama a nan ne saboda talauci da karancin damar da ke akwai a Arewa.
“Amma duk da haka, mutanenmu da yawa sun bar nan sun koma Arewa da zama.
“A da akwai ’yan Arewa da ke zaune a kauyukan Kudu maso Gabas suna harkar tireda da kananan sana’o’i kamar fawa da gyaran takalma da sauransu, amma yanzu sun yi kaura saboda ayyukan IPOB; abin ya kara muni a baya-bayan nan.”
Ya ce, “Mun ji dadin yajin aikin da ’yan kasuwar Arewa suka shiga domin zai isar da sako ga gwamnoni da sarakunan gargajiya a yankin Kudu maso Gabas su yi abin da ya kamata tare da kare rayukan ’yan uwanmu.
“Mun ji dadi da Gwamnatin Tarayya ta tura sojoji su yi maganin su, ya kamata a hukunta su; idan har za a iya bibiya a kamo wani matashi kan sakon da ya sa a Twitter ai babu abin da zai hana a kama wadannan masu kashe kashen.”
Abin ya kara muni
Wani mazaunin Jihar Imo, Muhammed Abdulkadir, ya ce kisan da ake wa ’yan Arewa a Kudu Maso Gabas a kullum ya kara tsanani
Ya ce, “Ko jiya (Laraba) sai da aka kashe mana wasu direbon manyan motoci da yaran motansu a lokacin da suke jigilar wasu kayan abinci a Idiato, kan titin Onitsha-Owerri.
“Haka kuma an tare wasu fasinjoji, aka kashe su, aka kona suka cikin motar.
“Da ni aka yi musu wanka, wadanda suka samu rauni kuma an kai su asibitoci.”
Ya ce gwamnan jihar Imo na taimaka musu da kudin jinyar marasa lafiyan, “amma shi ma ya fara gajiya.”
Don haka ya bukaci ’yan Arewa da suke zaune a kauyukan yankin su tashi, a matsayin matakin riga-kafi.
Ta bayyana cewa yajin aikin da ’yan kasuwar Arewa suka shiga zai taimaka wajen magance matsalar, “domin yanzu har wanda bai sani ba, zai sani kuma ya ji a jikinsa.
“Hakan zai sa shugabanni su yi abin da ya kamata; ko da yake mu ma ’yan Arewa da ke zaune a nan din za mu ji a jikinmu.”