✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

IPOB ta kona fadar basarake a Imo

Maharan sun bi lungu da sako suna neman basaraken kafin su kona gidansa.

Wasu maraha da ake zargi ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun kona fadar dabaraken al’ummar Etekwuru da ke Karamar Hukumar Ohaji/Egbema a Jihar Imo.

Maharan sun kuma banka wa motar basarken da sauran kadarorin da ke harabar gidan wuta, a lokacin farmakin da aka kai da tsakar dare.

Isar maharan gidan basaken ke da wuya, suka shiga menan shi a lungu da sako, amma da ba su same shi ba, sai suka banka wa gidansa wuta.

Majiyarmu ta ce a halin yanzu basaken ya samu mafaka a Babban Ofishin ’Yans anda da ke yankin Mmahu.

A ranar Alhdmis sojoji sun bindige wani da ake zargi mayakin kungiyar IPOB ne a wata musayar wuta da suka yi ga kungiyar. Soja daya ya kwanta dama a dauki ba dadin.