Wasu maraha da ake zargi ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun kona fadar dabaraken al’ummar Etekwuru da ke Karamar Hukumar Ohaji/Egbema a Jihar Imo.
Maharan sun kuma banka wa motar basarken da sauran kadarorin da ke harabar gidan wuta, a lokacin farmakin da aka kai da tsakar dare.
- Sojoji sun kashe sabon shugaban ISWAP, Malam Bako
- ‘Buhari ya ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda kawai’
Isar maharan gidan basaken ke da wuya, suka shiga menan shi a lungu da sako, amma da ba su same shi ba, sai suka banka wa gidansa wuta.
Majiyarmu ta ce a halin yanzu basaken ya samu mafaka a Babban Ofishin ’Yans anda da ke yankin Mmahu.
A ranar Alhdmis sojoji sun bindige wani da ake zargi mayakin kungiyar IPOB ne a wata musayar wuta da suka yi ga kungiyar. Soja daya ya kwanta dama a dauki ba dadin.