Al’ummar Hausawa a garin Orlu na Jihar Imo sun zargi jami’an tsaron haramtacciyar kungiyar kafa kasar Biafra (IPOB) da kashe Hausawa hudu a ranar Litinin.
Wani mazaunin garin Orlu da ya bukaci a kira shi da suna Yusuf saboda dalilan tsaro ya ce sai da jami’an tsaro suka kawo dauki kafin aka takaita kashe-kashen na IPOB a yankin.
- Kotu ta kwace kudaden tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari
- Buhari ya nada sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro
- An kone gidaje a artabu tsakanin jami’an tsaro da ’yan IPOB a Imo
“Kowanne daga cikin gawarwakin mamatan an gano shi ne a runfunan da yake kasuwanci,” inji shi.
Ya ce sojoji ne suka gano gawarwakin suka kuma mika su ga shugaban Hausawan garin, aka kuma yi musu jana’iza kamar yadda Musulunci ya tanadar.
Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun rasu sakamakon dauki ba dadin da sojoji da ’yan sanda suka yi da jami’an tsaron na IPOB a garin Orlu a ranar Litinin.
Yusuf ya ce: “Rikicin ya fara ne ranar Alhamis bayan mutane sun ki biyan harajin da IPOB ta sanya musu, wanda hakan ya fusata su suka je suka kone fadar Orlu Eze.”
Ya ambato cewa a lokacin tarzomar #EndSARS ma an kashe Hausawa sama da 40 a garin, kuma kafafen yada labarai sun bayar da rahoton amma babu matakin da aka dauka.