Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF), ta bayyana kisan tsohon Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa Goodluck Jonathan kan Harkokin Siyasa, Ahmed Gulak, a matsayin abin takaici mafi girma kuma abin Allah wadai.
A martaninsa game da kisan, Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ce abin bakin ciki ne kuma abun kyama.
- ’Yan sanda sun harbi Sowore a wurin zanga-zanga
- ’Yan sanda sun aika wadanda suka kashe Gulak lahira
- Harin Islamiyya: ’Yan bindiga sun sako kananan yara 11
“Mummunan abu ne wanda dole a yi tir da shi gaba daya,” inji shi.
Lalong ya ce dole ne a kalli kisan Gulak a matsayin laifi mafi muni, sannan ya yi gargadi cewa siyasantar da lamarin ka iya haifar da mummunan tashin hankali a kasa.
Ya ce rahoton da ’yan sanda suka bayar na ganowa da kuma kashe wadanda ake zargi da kisan marigayin dan siyasar, abun a yaba ne.
Shugaban kungiyar gwamnonin ya bukaci jama’a da su rika karfafa wa jami’an tsaro gwiwa don samun damar dakile ayyukan ta’addanci a Najeriya baki daya.
Ahmed Gulak ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama a Jihar Imo, inda ’yan bindiga da ake zargin ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne suka harbe shi har lahira, da safiyar ranar Lahadi.