✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPMAN ta yi barazanar ladaftar da mambobinta da suka saba doka

kungiyar Dillalan Man Fetur Masu Zaman Kansu reshen Jihar Neja ta yi barazanar ladaftar da duk wani mambanta da ya ki sayar da mai a…

kungiyar Dillalan Man Fetur Masu Zaman Kansu reshen Jihar Neja ta yi barazanar ladaftar da duk wani mambanta da ya ki sayar da mai a kan farashin da gwamnati ta sanya na Naira 145 a kowace lita.
Shugaban kungiyar a jihar, Alhaji Adamu Ahmed Erena shi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da manema labarai kan harkokin kungiyar.
Ya ce kungiyar za ta hada kai da hukumar lura da sayar da albarkatun man fetur wato DPR da kuma tawagar da ke sanya ido ga yadda ake sayar da mai don tabbatar da ganin ’yan kungiyar sun bi doka.
“Za mu hada kai da wadanda suke da ruwa da tsaki kamar hukumar DPR da tawagar da ke sanya ido kan yadda ake sayar da mai a jihar don mu tabbatar cewa kowa ya bi doka da oda na sayar da mai a kan farashin gwamnati,” inji shi
Ahmed Erena ya dora alhakin sayar da mai fiye da farashin gwamnati a kan ’yan bumburutu a jihar.
Ya ce ’yan bumburutu ko ’yan cuwa-cuwa ba mambobin kungiyarsu ba ne saboda haka ya ce ya kamata jama’a su bambance aya da tsakuwa.
Ya dage a kan cewa ’yan bumburutu na fakewa ne da sunan kungiyar dillalan man fetur domin su batawa kungiyar suna a idon jama’a.
Saboda haka sai ya ce za su yi amfani da dukkan damar da suke da ita wajen ganin sun kawo karshen sayar da man a kasuwannin bayan fage a jihar.
Shugaban wanda ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari na daukar matakan da suka dace a harkar man fetur, ya ce turbar da shugaban ya dauka za ta zama alheri ga ’yan Najeriya.
Ya ce matakan da shugaban kasa ya dauka ne suka zama sanadin wadatar mai a kasar nan.
Hakazalika, ya yaba wa Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello saboda namijin kokarin da ya yi na ganin mai ya wadata a jihar.
Ya ce Gwamnan shi ne na farko da ya yi kokarin ganin ’yan kungiyar sun samu mai daga daffo cikin sauki ba tare da wata matsala ba.
“Mu ne jiha ta farko da muka samu kashi 50 na man da aka tanadar mana a daffo kuma muka samu nasarar daukan man da raba shi a gidajen man jihar Neja sakamakon kokarin da gwamnanmu ya yi,” inji shi.
Daga nan sai ya ce kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin gwamnatin Shugaba Buhari ta cimma burin da ta sanya a gaba na wadata kasa da albarkatun man fetur.